2023: Mambobin PDP a Majalisar Tarayya sun goyi bayan Saraki a matsayin ɗan takararsu

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Shugaban Majalisar Dattawa na baya-bayan nan, Dr. Abubakar Bukola Saraki ya gana da gungun ‘ya’yan jam’iyyar PDP da ke majalisun tarayya da na Dattawa a ranar Talata da ta gabata, inda ya dace da samun tagomashin wani ƙuduri na majalisar wakilai da ta ɗabbaka shi a matsayin ɗan takarar neman shugabancin ƙasa a zaɓen shekara ta 2023.

Duka tarurrukan guda biyu an gudanar da su ne a gidajen shugabannin marasa rinjaye biyu na majalisun, Sanata Enyinnaya Abaribe da Hon. Ndudi Elumelu baki ɗaya.

A yayin ganawar sa da ‘yan majalisar wakilai, wani mamba daga cikin gungun ‘yan jam’iyyar ta PDP ya gabatar da ƙudurin amincewa da Saraki a matsayin ɗan takarar sun a neman shugabancin ƙasa.

Ƙudurin, wanda ya samu goyon bayan wani mamba ɗan jam’iyya, shugaban marasa rinjaye na majalisar, Hon. Elumelu ya nemi kaɗa ƙuri’a ta hanyar jin sauti, yayin da ɗaukacin mambobin suka kaɗa bakunan su da cewa ‘Yayyy.

Da yake kuma yin jawabi ga dattawa na babbar majalisar, Saraki ya ce “gani a cikin dangi, domin dukkan mu ‘yan gida ɗaya ne. Dukkan mu mun jajirce wa tabbatuwar haɗin kan majalisa, da kuma kare ko kiyaye kundin tsarin mulkin ƙasar nan.

“Wannan shi ne dalili da ya sanya nake neman goyon bayan ku, kuma Ina so ku duba wannan lamari da idon basira, bisa ƙwazo, da sadaukantar da kai domin cimma wannan manufa.

“Nijeriya tana buƙatar tsayayyen shugaba wanda zai taɓuka abin kirki. Shugaba da zai wakilci ƙasar sa a kowane irin mataki da ‘yan ƙasa za su yi alfahari da shi, inji ɗaya daga cikin waɗanda suka mayar da jawabi kuma tsohon gwamnan jihar Benue, da yake wakiltar Mazaɓar sanata ta Arewa-maso gabacin Benuwai a majalisar qasa, Gabriel Suswam ya bayyana cewar, Saraki shugaba ne irin wannan ‘yan Nijeriya suke buƙata a wannan hali na tsaka-mai-wuya.

Wasu sanatocin, da suka bayyana Saraki a matsayin mutum haziƙi sun haɗa da Sanata Chukwuka Utazi, Sanata Matthew Urhoghide, Sanata Abba Moro, Sanata Kola Balogun da Sanata Jeff Orkar, da dai sauransu.

Tunda farko a wannan ranar, an samu wasu gungun matasa masu zurfin ilimi kan sana’o’i, haɗi da ‘yan kasuwa, waɗanda suka saya wa Saraki takardun nuna sha’awa dana tsayawa takarar shugabanci ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar su ta PDP, da gwamatsin shugaban jihar Kwara na jam’iyyar PDP, shugabar mata ta jam’iyyar, sakataren watsa labarai da wasu jiga-jigan jam’iyyar, waɗanda tare aka je dasu wajen sayen takardun.

Gungun masu yi wa Saraki yaƙin neman zaɓe, ƙarƙashin jagorancin Farfesa Iyorwuese Hagher su ma a gefe guda suna kan ziyara zuwa jihohi suna faɗakar da masu ruwa da tsaki da jiga-jigan jam’iyyar PDP kan aniyyar ta Saraki na shiga takarar neman shugabancin qasa, waɗanda a halin yanzu sun gama karaɗe shiyyar Arewa maso gabashin ƙasar nan da kuma Kudu maso yammaci.