2023: Masu shirin tafka maguɗi ku fice daga Binuwai ko ku kuka da kanku – Gwamna Ortom

Gwamna Samuel Ortom na jihar Binuwai ya yi gargaɗin cewa masu shirin tafka maguɗin zabe a 2023, mafi alheri a gare su shi ne su fice daga jihar ko kuma su kuka da kansu.

Ortom ya yi wannan gargaɗi ne yayin wata tattaunawa da manema labarai a Makurɗi bayan da ya dawo daga taronsu na Ƙungiyar Gwamnonin PDP da suka gudanar a Abuja.

A cewar gwmnan, “Ina tuanin cewa a matsayinmu na ƙasa mun samu cigaba, bai kamata mu koma rayuwa irin ta da ba alhalin duniya baki ɗaya ta bunƙasa.”

Ya ci gaba da cewa wajibi ne Shugaban Ƙasa ya sake tunani. Tare da cewa, yana mai bai wa Shugaban shawarar da kada ya sanya hannu a sha’anin yi wa Dokar Zaɓe kwaskwarima ba tare da saka batun yin amfani da na’ura wajen tattara bayanan zaɓe a cikin dokar ba.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Ortom na cewa, “Mu a nan jiharmu (Binuwai) za mu zama a shirye, duk wanda ya shigo don tafka maguɗin zaɓe a 2023, ya yi addu’arsa ta ƙarshe. Bai yiwuwa ka yi maguɗi a inda mu ke da rinjaye.”

A hannu guda, da yake maida martani kan kalaman gwamnan, Sakataren Hulɗa da Jama’a na jam’iyyar APC a jihar, James Ornguga, ya ce gwamnan da ilahirin jama’arsa babu abin da suka sani face maguɗin zaɓe. Tare da cewa, APC ta shirya masa a wannan karon.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *