Daga JOHN D. WADA a Lafiya
Ƙungiyar Ƙwararrun Matan APC na Ƙasa wadda aka fi sani da APC Professional Women Council of Nigeria a turance reshen Jihar Nasarawa ta tabbatar wa gwamnan jihar injiniya Abdullahi Sule cikakken goyon bayanta ɗari bisa ɗari don samun nasarar sa karo na biyu a zaɓen gwamnoni na shekarar 2023 dake zuwa.
Kodinitar ƙungiyar a jihar Kwamared Hajiya Halima Haruna Kunza ce ta bayyana haka a jawabin ta a wajen wani gangamin wayar da kawunan al’umma da neman goyon baya wa gwamnan wanda ƙungiyar ta shirya ta gudanar a cibiyar matasa na Ibrahim Abacha dake Lafiya babban birnin jihar.
Kwamared Halima Haruna Kunza ta ce ƙungiyar wadda ta ƙunshi mata ma’aikata dake aikin gwamnati da waɗanda ke zaman kansu a ɓangarorin rayuwa daban-daban a jihar sun yanke shawarar gudanar da taron ne don jawo ra’ayin sauran mata ‘yan uwan su da matasa da sauran al’umma baki ɗaya don su sake zabi gwamna Abdullahi Sule mai ci yanzu a matsayin gwamnan jihar karo na biyu a inuwar Jam’iyyar APC bayan sun yi la’akari da ɗimbin ayyukan cigaba da more rayuwa da gwamnatin sa ke cigaba da gudanarwa a jihar.
A cewar ta Jam’iyyar APC musamman a jihar ta kasance jam’iyya dake tafiya da mata a harkokin ta idan aka yi la’akari da yawan mata da take naɗa musu muƙamai daban-daban.
Saboda haka a cewarta mata a jihar ba su da wani zavi illa su yi duka mai yuwa don tabbatar da nasarar gwamnan da sauran ‘yan takara a inuwar APC a jihar da ƙasa baki ɗaya a zaɓukan 2023.
Ta ce wannan gangamin somin-taɓi ne don mata a jihar za su cigaba da gudanar da ire-iren sa nan gaba har sai sun cimma burin nasu.
Kodinetar ta cigaba da bayyana cewa, “Ina kuma so in yi amfani da damar nan don in yaba wa Maigirma Gwamna Abdullahi Sule dangane da namijin ƙoƙari da yake yi don tabbatar da zaman lafiya a faɗin jihar nan baki daya don kare rayuka da dukiyoyi inda a koyaushe yana bada fifiko ne ga fannin,” inji ta.
A nasa ɓangaren da yake maida martanin jawabi gwamnan jihar injiniya Abdullahi Sule wanda mai taimaka masa na musamman a fannin yawon buɗe ido da shaƙatawa Mista Moses Atondo ya wakilta ya gode wa ƙungiyar ta matan APC ma’aikata a jihar dangane da karamci da goyon baya da suka nuna masa a idon duniya baki ɗaya, inda ya tabbatar musu cewa wannan hakar su na tabbatar da nasarar sa karo na biyun ba zai tafi a banza ba.
A cewar sa hakan zai kuma sa gwamnatin sa ta cigaba da yin tafiya da su don cimma buƙatun su da sauran su.
Sauran manyan baƙi da suka yi jawabi duk sun yaba wa ƙungiyar dangane da matakin da suka ɗauka inda suka bayyana cikakken goyon bayansu ga ƙungiyar.