2023: Matasa sun buƙaci Tinubu ya fito takarar shugaban ƙasa

Daga WAKILINMU

Mambobin Ƙungiyar Matasa Magoya Bayan Tinubu (NYMT), sun yi kira ga jigon jam’iyyar APC, Asiwaju Ahmed Tinubu, da ya fito takarar neman shugabancin ƙasa a 2023.

Matasan sun yi ra’ayin cewa babu wanda ya fi cancanta ya gaji Shugaba Muhammadu Buhari kamar Tinubu domin ci gaba ƙarfafa nasararorin da gwamnatin APC ta samu.

A cikin wata sanarwar manema labarai da ya fitar a Abuja, Darakta Janar na ƙungiyar, Mukhtar Husseini ya jigon ya yi sadaukarwa sosai wajen ɗorewar dimukraɗiyyar da ake cin moriyarta a yau.

Ya ce buƙatar mara wa Tinubu baya ta taso ne bisa la’akari da makoma da kuma cigaban ƙasa a gaba, inda ya ƙara da cewa dattijon na da kamannun da ke tabbatar da zai iya hayewa da ƙasar nan tudun mun tsira.

Ya ci gaba cewa, nasarorin da Tinubu ya samu a lokacin da ya mulki Jihar Legas, alama ce da ke nuna yadda Nijeriya za ta samu bunqasa muddin aka zaɓe shi anmatsayin Shugaban Nijeriya a 2023.

Sanarwar ta ce, “Muna kira ga Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da ya fito takarar shugaban ƙasa a 2023 don amfanin ƙasa da kuma dimukraɗiyyarmu.

“Ko shakka babu muna da yaƙinin cewa shi ne ya fi cancanta ya gaji Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari duba da irin ayyukan cigaba da ya yi a gwamanti da makamacin haka.”