2023: Matashi ya fi cancanta da mulkin Nijeriya – IBB

A cikin wata wasiƙa da Tsohon Shugaban Ƙasa, Ibrahim Badamasi Babangida (IBB), ya aika wa jagoran APC, Bola Tinubu, da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya jaddada musu cewa Nijeriya ta fi buƙatar matashin shugaba a 2023.

Haka ma, ko a wata hira da aka yi da shi a tashar ARISE TV a Juma’ar da ta gabata, an ji Babangida ya ce, “Na soma hanƙoron matashin shugaba a Nijeriya.”

Ya ce, “Na riga da na ga mutum ɗaya ko biyu ko uku daga irin waɗannan matasa, na yi imanin za su iya muddin za mu jawo su.”

Atiku da Tinubu dukkansu dattawa ne masu kwaɗayin mulkin Nijeriya, lamarin da wasu ke ganin sun riga sun tsufa, kasancewar Atiku ya kai shekara 70, yayin da Tinubu ke shirin cika shekara 70 da haihuwa ya zuwa 2022.

IBB ya lissafo wasu siffofi da suka dace a gan su tattare da shugaba nagari da suka haɗa da zama mutum da ya zagaya sassan duniya, ya zamana mai haƙuri, ya zama mai so sassan ƙasa da sauransu.

Tsohon shugaban ya soki gwamnatin Buhari da rashin tsaro da talaucin da ba a taɓa gani ba a ƙasa.

Wasu na ra’ayin cewa duba da yadda Buhari ke fama da lafiyarsa saboda yawan shekarunsa da kuma sanyar da yake da ita wajen ɗaukar mataki, ya sa ake ganin gara mulkin ƙasa ya koma hannun matashi ya zuwa 2023.