2023: Mu guji ra’ayin ƙabilanci da addini, inji Ƙungiyar Nijeriya Ɗaya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja

Ƙungiyar Nijeriya Ɗaya (ONG), wata ƙungiya mai zaman kanta ta ‘One Nigeria Group’, ta yi kira ga ’yan Nijeriya da su guji ra’ayin ƙabilanci da addini, su zaɓi ɗan Nijeriya mai kishin ƙasa a zaɓen Shugaban Ƙasa na 2023.

Shugaban ƙungiyar, Alhaji Muhammad Saleh-Hassan, ne ya yi wannan roƙo a wata sanarwa da ya fitar a Abuja cikin makon nan.

Saleh-Hassan ya buƙaci ’yan Nijeriya da su zaɓi shugaban ƙasa wanda ya kamata ya zama shugaban ƙasa ba tare da la’akari da ko wane yanki na ƙasar ya fito ba.

Ya buƙaci ’yan Nijeriya masu kishin ƙasa da su shirya katin zaɓe na dindindin kafin zaɓen 2023, domin su zavi shugaban qasa mai kishin qasa daga ko ina a faɗin ƙasar nan.

“Saboda haka, ina kira ga ɗaukacin ’yan Nijeriya, kasancewar zaɓen 2023 ya kusa, a matsayinku na ’yan Nijeriya masu kishin ƙasa, ku je ku karɓi katin zaɓe ku zaɓi shugaban ƙasa mai cikakken iko na Nijeriya daga kowane yanki na ƙasar nan.

“Yana da kyau mu tuna cewa ƙabilanci da addinanci na kashe ƙasarmu fiye da cin hanci da rashawa.
“A yau, ra’ayin ƙabilanci ya haifar da ƙungiyar IPOB, Boko Haram, ’yan bindiga da sauran masu aikata laifuka a faɗin ƙasar nan.

“Musamman a Kudu maso Kudu, waɗannan abubuwa suna yin zagon ƙasa ga tattalin arzikin ƙasa, don haka suke sace miliyoyin ganga na ɗanyen mai,” inji shi.

Shugaban ƙungiyar ya yi kira ga ɗaukacin ’yan Nijeriya masu kishin ƙasa da su haɗa ƙarfi da ƙarfe da ƙungiyar domin kawar da kyama da ƙabilanci da addinanci, inda ya ƙara da cewa, ƙarfin Nijeriya ta dogara ne da bambancinta.

“Bari mu tashi tsaye domin yaƙar ’yan ta’adda da maƙiya Nijeriya, masu ƙoƙarin gurgunta tattalin arzikinmu, da neman cinna wa ƙasarmu wuta.

“Zaɓen zai zo cikin kwanciyar hankali ba tare da tashin hankali kafin zaɓe ko bayan zaɓe ba, kuma maƙiyan ƙasarmu za su binne kawunansu da kunya.

“Ya kamata mu yi koyi da rikicin Ukraine kuma mu fara son ƙasarmu, mu kare ƙasarmu da dukkan ƙarfinmu kamar yadda muka yi alƙawari,” inji shi.

Saleh-Hassan ya yi nuni da cewa, a tsawon shekaru, ra’ayoyin ƙabilanci da na addini da kuma aikata laifukan da aka aikata ba su wuce kawai cikin zafi da wahala ga ƙasar da ’yan ƙasar ba.

“Waɗannan ba abin da suka kawo wa ƙasar nan sai zafi da kowane irin mugunta da suka haifar da zawarawa, marayu da yara ba tare da makaranta ba.

“Ba mu da wata ƙasa face Nijeriya, mu kuma tuna cewa babu wata kasa a duk faɗin duniya da za ta iya ɗaukar ’yan gudun hijira miliyan 200 waɗanda za su iya neman mafaka idan abin da ba zato ba tsammani ya faru,” inji shi.

Ƙungiyar ta kuma yi Allah wadai da duk wasu hare-haren ’yan bindiga da ke faruwa a ƙasar tare da yin kira ga jami’an tsaro da su ci gaba da yin iyakacin ƙoƙarinsu wajen ganin an hukunta duk wani mai laifi da ’yan aware.

Sanarwar ta kuma ruwaito Sunday Attah, kodinetan ayyukan ƙungiyar, wanda ya yi kira ga masu fasaha da mawaƙan Nijeriya da su yi Allah wadai da ayyukan sace-sacen Boko Haram ta hanyar kaɗe-kaɗe da aikinsu.

Sanarwar ta qara da cewa, “dole ne su tashi tsaye don nuna adawa da duk wasu ayyukan da za su yiwa ƙasar suna.”