2023: Na fi kowane ɗan takara cancantar zama shugaban ƙasa — Ngige

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ministan Ƙwadago da Samar da Ayyuka, Chris Ngige, ya bayyana cewa ba ma a jam’iyyar APC ba kaɗai, hatta ‘yan jam’iyyar adawa sun san shi ya kere sauran masu son tsayawa takarar shugabancin ƙasar nan a cancanta.

Ofishin yaɗa labarai na Ngige, a cikin wata sanarwa ranar Litinin ya ce Ngige ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke jawabi ga magoya bayansa a Amansea, wani gari mai iyaka da jihar Enugu bayan ya ziyarci Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi.

Sanarwar ta ƙara da cewa Ngige ya ba da bayaninsa na tuntuɓar jam’iyyun siyasa na adawa a lokacin da ya yi jawabi ga magoya bayansa a garin Amansea da ke kan iyaka da jihar Enugu bayan ya ziyarci Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi.

Ofishin yaɗa labaran ya kuma bayyana cewa Ngige na da wannan yaƙini ne bayan da ya fahimci cewa har sauran jam’iyyu ma a na ƙaunar sa.

“Na ziyarci gwamnan jihar Enugu ne a wani ɓangare na tuntuvar da nake yi a fadin ƙasar nan. Duk da cewa yana PDP, ɗan ƙabilar Igbo ne.

“Shi mutum ne mai gaskiya, mai kuma fahimta. Kar ku manta kuma Enugu ce babban birnin tsohon yankin Gabas. Kuma ka san cewa mu na mutunta juna ne.

“A cikin makon nan, na kuma tuntuɓi wasu ‘yan Nijeriya da ba su da alaƙa da wata jam’iyyar siyasa. Don haka sai na tuntuɓi Gwamnan Jihar Enugu kan aniya  ta tsayawa takara da kuma neman ra’ayinsa ma.

“Don haka wannan tafiya ba ta ‘yan APC kaɗai ba ce. ‘Yan uwanmu a PDP sun amince da cewa na fi wasu masu neman muƙami a jam’iyyarsu,” in ji shi.