2023: Nijeriya za ta fuskanci ƙalubale mai tsanani fiye da 2015 – Sanusi

“Dole bakiɗayanmu mu kasance cikin shiri saboda tsauraran matakan da za a ɗauka, muddin kuma aka ɗauki matakan sai mun ɗanɗani kuɗarmu”

Daga BASHIR ISAH

Yayin da zaɓuɓɓukan 2023 ke ta ƙaratowa, Sarkin Kano na dauri, Muhammadu Sanusi II, ya ce Nijeriya na rayuwa ne a kan siraɗi wanda akwai yiwuwar ƙasar ta fuskanci ƙalubalai masu tsanani daga shekarar 2023.

Sanusi ya yi wannan furuci ne a wajen taron karrama shi da al’ummar Musulmin Egba a Abeokuta suka shirya masa a ranar Litinin da ta gabata.

A cewar Sanusi, “Magana ta gaskiya, muna rayuwa ne a kan siraɗi. A 2015 mun faɗa a wani wagegen rami, a 2023 kuwa za mu faɗa a ramin da ya ɗara na 2015 zurfi.

“Ina fatan masu fafutukar neman shugabancin ƙasa suna da fahimtar cewa matsalolin da za su fuskanta sun ninka waɗanda aka fuskanta a 2015. Dole bakiɗayanmu mu kasance cikin shiri saboda tsauraran matakan da za a ɗauka, kuma muddin aka ɗauki matakan sai mun ɗanɗani kuɗarmu.

“Mafitar ba shi ne kowannenmu ya faɗa cikin siyasa ba, ƙasar nan na buƙatar nagartattun ‘yan siyasa. Abin da muke buƙata shi ne limamai da fastoci da bishop-bishop waɗanda za su tashi su tunatar da ‘yan siyasa game da tsoron Allah.

“Akwai buƙatar masu tsattsauran ra’ayi waɗanda za su riƙa suka ga harkokinsu. Akwai buƙatar sarakuna waɗanda za su zame wa al’umma murya. Kowa na da rawan da ya kamata ya taka, sannan mu taka rawan gwargwadon iko.”

Haka nan, tsohon shugaban CBN, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su duƙufa da addu’a don samun shugabannin ƙwarai a dukkanin matakai.

Kazalika, ya gargaɗi’yan ƙasa kan su zaɓi shugabanni bisa cancanta waɗanda za su shayar da su romon dimukuraɗiyya yadda ya kamata. Kana su yi hattara da zaɓen mutanen da za su ruɗe su da kuɗi da kyuatuttuka ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *