2023: Okorocha ya ɗauri niyyar takarar shugaban ƙasa

Daga BASHIR ISAH

Sanata Rochas Okorocha na jam’iyyar APC daga jihar Imo, shi ma ya bi sahun masu kwaɗayin mulkin Nijeriya ya zuwa 2023.

Okorocha wanda shi ne sanata mai wakiltar Imo ta Yamma a Majalisar Tarayya, ya bayyana muradinsa na takarar shugaban ƙasa ne cikin wata wasiƙa da ya aike wa Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmed Lawan inda shi kuma ya karanto wasiƙar yayin zaman majalisar a jiya Laraba.

Sanatan ya ce yana da shirin da zai yi hira da ‘yan jarida ran 31 ga Janairu a Babban Zauren Taro da ke Abuja don bayyana wa duniya ƙudirin nasa.

Da wannan, ya tabbata cewa Sanata Okorocha ya zama ɗaya daga jerin waɗanda ke niyyar yin takarar shugaban ƙasa daga shiyyar Kudu-maso-gabas a 2023 idan Allah Ya kai mu.