2023: Sai da haɗin kai APC za ta ƙwaci mulki a hannun PDP a Taraba, cewar Ɗan Atiku

Daga ABUBAKAR A. BOLARI, a Gombe

An bayyana cewa muddin aka samu haɗin kan da ya kamata, cikin ruwan sanyi APC za ta karɓe mulkin Taraba daga hannun PDP a 2023.

Bayanin haka ya fito ne daga bakin jigo a APC a jihar Taraba kuma mai neman shugabancin APC na jihar, Muhammad Ɗan Atiku Jalingo, yayin wata tattaunawa da ya yi da manema labarai kwanan nan a Gombe domin nuna sha’awarsa ta neman jagorancin APC ta Taraba.

Ya ce rashin shugabanci nagari da rashin mutunta jama’a ne yasa APC ta faɗi zaɓe, amma tun da yanzu al’ummar Jalingo sun gane PDP ba ta taɓuka komai ba idan suka gyara za su ƙwace mulkin cikin sauƙi.

Ya ƙara da cewa yana da kishin jami’yyarsu a ransa, kuma faɗuwar jami’yyar a zaɓe ya dame shi don haka ya fito neman wannan kujera don ceto APC da al’ummar Taraba daga mulkin mallaka.

A cewar sa muddin aka zaɓe shi ya zama shugaban jam’iyyar na jihar Taraba zai bi kan masu ruwa da tsaki na jihar tun daga matakin unguwanni zuwa ƙananan hukumomi da jiha ya nemi haɗin kansu don ceto talakawanTaraba.

A ƙarshe, ya yi kira ga ‘yan jami’yyarsu ta APC da cewa su ba shi haɗin kai da cikakken goyon baya domin a gudu tare a tsira tare.