2023: Sarkin Musulmi da CAN sun rattaɓa hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III, da Ƙungiyar Kiristoci ta Nijeriya (CAN) sun rattaba hannu a wata yarjejeniyar zaman lafiya gabanin babban zaɓen 2023.

Yarjejeniyar dai ana sa ran ta samar da zaman lafiya da kawar da fitina ta fuskar addini a lokacin zaɓen na baɗi.

Manyan masu faɗa a jin biyu sun sa hannu ne a wani taron ƙoli na qasa da ƙasa kan wanzar da ’yancin addini da wata gidauniyar samar da zaman lafiya da haɗin gwiwar wasu ƙungiyoyin kare haƙƙin bil adama guda 70 suka shirya.

An gudarnar da taron ne a birnin Washington na ƙasar Amurka.

A wata sanarwa da CAN ta fitar a ranar Laraba a Abuja wacce Shugabanta, Ayokunle ya sanya wa hannu ta ce, vangarorin biyu sun yi alƙawarin yin aiki tare da guje wa tashi hanakali.

Sun kuma amince su rungumi tattaunawa tare da gina mabiyansu a kan haƙuri da juna domin wanzar da zaman lafiya.

“Na san akwai Musulmi da Kiristoci ’yan Nijeriya da yawa da ke kyamar tashin hankali, kuma suke buƙatar samar da zaman lafiya su da ’yan uwansu da kuma dangi kamar yadda mu ke a da,” inji Ayokunle na ƙungiyar CAN.

Sanarwar ta kuma ce ƙungiyar da kuma Sarkin Musulmin za su yi tsayuwar daka don ganin an yi zaɓe na gari mai cike da adalci.