2023: Sauya fasalin Naira da ƙarancin fetur ba za su hana nasarata ba – Tinubu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a ƙarƙashin Jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya yi zargin matsalar ƙarancin man fetur da ake fuskanta da sauya fasalin wasu takardun Naira da aka yi, take-taken neman wargaza zaɓen 2023 ne kawai.

Tinubu ya bayyana haka ne yayin gangamin yaqin neman zaɓen APC da ya gudana ranar Laraba a Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun.

“Ba sa son zaɓen ya gudana. So suke su wargaza shi. Za ku bari hakan ta faru?” inji Tinubu.

Ɗan takarar ya ce, yana da yaƙinin matsalar ƙarancin fetur ba za ta hana ’yan Nijeriya zuwa kaxa ƙuri’a ba ranar zaɓe.

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC ya kuma yi alƙawarin bayar da rance ga ɗalibai idan aka zave shi, inda ya ƙara da cewa “babu wanda zai kasa shuga jami’a saboda kuɗin makaranta.”

Tinubu ya ɗauki lokaci ya godewa al’ummar jihar bisa goyon bayan da suka ba shi. Ya kuma tunatar da yadda ya furta a yayin da ake ci gaba da gudanar da babban taron shugaban ƙasa na jam’iyyar APC a watan Yunin bara a Abeokuta cewa lokaci ya yi da ya zama shugaban Nojeriya da kuma yadda a ƙarshe ya lashe tikitin jam’iyya mai mulki duk da tsananin adawa.

Tinubu ya halarci taron ne tare da Gwamna Dapo Abiodun wanda ke neman sake tsayawa takarar gwamnan Ogun; Shugaban hukumar kula da wuraren shaƙatawa na jihar Legas, Musiliu Akinsanya, wanda aka fi sani da MC Oluomo, da sauran jiga-jigan jam’iyyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *