2023: Wike ya ɗauki alƙawarin taimakawa a saki Inusa Yellow

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnan Jihar Ribas kuma mai neman takarar shugabancin ƙasa a jam’iyyar PDP, Nyesom Wike, ya yi alƙawarin yin iya bakin ƙoƙarin sa don ganin an saki Yunusa Dahiru, wanda aka fi sani da Yellow, a gidan yari a Jihar Bayelsa.

Manhaja ta tuna cewa wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Yenagoa, Jihar Bayelsa, a 2020, ta yanke wa Yunusa Yellow hukuncin ɗaurin shekaru 26 a gidan yari bisa samunsa da laifin safarar yara da kuma lalata da wata yarinya mai suna Ese Oruru.

An zargi Yunusa Yellow, a 2015, da yin garkuwa da Oruru a Bayelsa, ya kawo ta Jihar Kano, inda a ka ce ya yi auren dole da ita har ma ya yi mata ciki, lamarin da a lokacin ya haifar da cece-kuce tsakanin ‘yan Arewa da Kudancin ƙasar nan.

Sai dai kuma Wike, wanda ya yi wannan alƙawari a Kano, bayan buƙatar da shugaban jam’iyyar PDP, reshen jihar Kano, Shehu Sagagi ya miƙa masa ta taimaka wa a saki Yellow, ya ce a ba shi cikakken bayani domin sanin ta inda zai shiga maganar.

Sagagi, a cikin jawabin maraba, ya buƙaci Wike, wanda ya kawo masa ziyara, a madadin al’ummar Kano, da ya taimaka wa Yellow da ke tsare a gidan yari ya samu ya fita.

Sagagi ya ci gaba da cewa, “Kano ta damu da wasu abubuwa da suka kai ga yanke wa ƙaninmu Yunusa Dahiru hukunci, kuma mun yi Allah wadai da cin mutuncin da ake yi masa a gidan yari.

“Dangane da haka, muna roƙon gwamna da ya sa baki a kan wannan al’amari saboda ya damu al’umma a nan Jihar Kano.”

A martanin da Wike ya mayar, ya buƙaci cikakken bayani kan samun kundin shari’ar ta Yellow  tare da tabbatar wa jiga-jigan jam’iyyar PDP na Kano a shirye ya ke ya yi duk mai yiwuwa bisa manufar doka don yin adalci.