2023: Yadda Mohammed Malagi ya mayar da APC tsintsiya maɗaurinki ɗaya a Jihar Neja

Daga AMINA YUSUF ALI
 
A kwanakin nan ne dai Shugaba kuma Mawallafin rukunin kamfanin jaridun Blueprint da Manhaja, Alhaji Mohammed Idris Malagi (MIM), ya kai wata ziyara zuwa reshen Jam’iyyar APC na Jihar Neja a Minna, Babban Birnin Jihar.

Wakilinmu ya rawaito cewa, wannan ziyara ta Kakakin Nufe ta buɗe wani sabon shafi a kan muradinsa na nuna sha’awarsa ga takarar Gwamnan Jihar Neja a kakar zaɓe mai zuwa ta 2023. 

Shigowar uban gayya:
Da ƙarfe 7 na safiyar ranar Talatar, wato daidai da 22 ga watan Fabrairu shekara ta 2022, ƙofar shiga garin Minnan jihar Neja ta ɗinke da cincirindon ‘yan jam’iyyar APC da kuma ‘yan uwa da masoya da magoya baya, domin tarben Mawallafin jaridun Blueprint da Manhaja, Mohammed Idris Malagi, wanda ya kawo ziyara ga uwar Jam’iyyar APC a sakatariyar jam’iyyar ta jihar.  Daga nan kuma Malagi ya bayyana tare da tawagarsa, inda waje ya ƙara kacamewa da ife-ife da sowar murna har ma da waƙe-waƙe da kirari. Daga nan aka dafe masa baya aka yi masa rakiya i zuwa ofishin jam’iyyar APC ta jihar Neja. A dai-dai wannan lokaci su ma shugabanni jam’iyyar da sauran magoya baya su ma suka yi cikar farin ɗango kamar su shugabannin jam’iyyar na ƙananan hukumomi, Wuman Lidoji, shugabannin matasa da sauran masu ruwa da tsaki dukka a ƙarƙashin shugabancin shugaban jam’iyyar na jiha, Zakari Jinkantoro, suka zo suka tarbi mawallafin Blueprint ɗin wanda shi ne Kakaki Nufe. 

Tarbar girmamawa:
Rahotanni sun nuna cewa, Malagi ya samu tarba ta hannu bi-biyu daga al’ummar jihar Neja. Domin masana da masu sharhi kan al’amuran siyasar jihar sun bayyana cewa, ba a taɓa samun taron da al’ummar jihar suka fito ƙwansu da ƙwarƙwatarsu ba kamar wannan na ɗan takarar Gwamnan jihar, Kaakaki Nufe. Kai ka ce taron kamfe ne na shugaban qasa. Kodayake, Ɗan takarar gwamnan bai zo da nufin yin kamfe na siyasa ba. Ya zo ne ziyara ga sakatariyar jam’iyyar ta jiha.  Amma kan ka ce kwabo, waje ya kacame. Nan taron ya koma tamkar gangamin siyasa. 
A yayin da Kaakaki Nufe  ya isa sakatariyar jam’iyyar APC, fastocin takararsa na gwamnan jihar Neja a 2023 sun cika ko’ina ba masaqa tsinke a garin Minna. Masu sharhi a kan al’amuran siyasa sun bayayana cewa, wannan kaɗai ta isa ta nuna cewa, Kaakaki Nufe shi ne ɗan takararar Gwamna da ake sa ran zai doke sauran ‘yan takarar gwamnoni. Domin kuwa ya mamaye zukatan al’ummar garin bakiɗaya. 

Ɗaya daga cikin magoya bayan jam’iyyar APC kuma ɗan gani kashe nin Malagi, Muhammad Yusuf ya bayyana wa wakilin Blueprint cewa, “mun yi tsananin farin ciki da zuwan gwamnanmu na shekara ta 2023 mai zuwa Insha’Allahu. Mun daɗe muna kiransa da ya zo ya tsaya takara”.

Ya ƙara da cewa, “A yau ina cike da farin ciki domin ya amsa kiranmu don ya zo ya hidimta. Kamar yadda kake gani a yanzu, ya ishe ka gane irin farin jinin da Malagi yake da shi a jihar Neja”.

Haka wata mamallakiyar gidan cin abinci a jihar mai suna, Madam Peace ta bayyana cewa, a yau ta samu ciniki mai yawa saboda taron da aka yi na tarar ɗan takararar. Abinda a cewar ta ya sa ta ji zumuɗin son ganinsa. Inda ta hange shi a cewar ta ganshi kyakkyawa ne mai haiba, kuma mai cikar kamala fiye da sauran ‘yan takarar da ta ce ba abinda suka iya sai surutu a jihar. Sannan ta yi fatan ‘yan siyasa za su ba wa Malagi goyon baya domin ya zama Gwamnan Neja a 2023.

Taron jam’iyya:
Daga shigowar Malagi babban ɗakin taron jam’iyyar, sai mutane suka sake tururuwar bin sa. Mutane suka yi cikar kwari a ɗakin. Har ma suka ninka yawan mutanen da ɗakin ya kamata ya ɗauka sau uku. Shi kuma shugaban Jam’iyya na jiha, Jikantoro da sauran iyayen jam’iyya sun buɗe kunnuwa donjin saƙon mai gayya mai aiki. Malagi yana buɗe bakinsa bai yi jawabi a kan komai ba, sai a kan haɗin kan jam’iyyar APC. Da yadda za a ƙara ƙarfafata domin ta kai bantenta a kakar zaɓe mai zuwa ta 2023. 

Alhaji Malagi ya bayyana cewa: “Bayan gaisuwa ga shugaban Jam’iyya da iyayen jam’iyya bakiɗaya, ina goyon bayan jam’iyyar APC a jihar Neja ne domin na lura cewa, jam’iyya ce ta (cigaban ) al’umma. A don haka nake mata tabbacin nasara a kowanne mataki, sannan zan cigaba da tallafa wa al’amurranta a duk lokacin da aka buƙaci na yi hakan”.  

A take a nan kuma Malagi ya nuna irin nasa salon siyasar. Wato shi da gamo da kasawa ne. Sannan sha yanzu, magani yanzu ne kuma. Ba irin ‘yan siyasar da sukan yi alƙawari ya bi ruwa ko shanun sarki ba ne. Ko da ya buɗe tsarabar da yake tafe da ita ga jam’iyya, nan da nan waje ya ruɗe, ba abinda kake ji sai sowa da kiran sunan Malagi tare da yi masa kirari da yabo.  

Bayan hayaniyar ta lafa, sai Malagi ya gyara murya ya ce: A wannan gaɓa ina neman dama don na miƙa ɗan ƙaramin tallafina don cigaba da haɗin kai, da kuma bunƙasar jam’iyyar kamar haka: “

Malagi ya ba da jimillar motoci 31 ƙirar Sharon, sai kuɗi Naira miliyan 43 duk a matsayin tallafi ga jam’iyyar APC. Wato motoci guda uku da Naira miliyan 15, ga sakatariyar jam’iyyar ta jiha. Su kuma rassan jam’iyyar na yankuna uku na jihar za su samu motoci guda-guda da Naira Miliyan guda kowannensu. Sannan ofisoshin jam’iiyyar na  ƙananan hukumomin jihar guda 25 za su samu motoci ɗai-ɗai da miliyan guda-guda kowannensu. Bayan rarraba wannan tsaraba, Jikantoro ya samu muryarsa da ƙyar kuma ya yi godiya ga Malagi. Ya ƙara da cewa, wannan abu da Malagi ya yi ba ƙaramin ƙarfafa jam’iyyar APC zai ƙara yi ba a jihar. 

Ƙaddamar da takarar 2023:
Duk da dai mun ji muradin son Malagi da manufarsa ta son tsayawa takarar Gwamna a kakar zaɓe mai zuwa ta 2023, amma ba mu ji inda basaraken ya buɗe baki ya bayyana aniyarsa na tsayawa takarar gwamnan ba. Kamar yadda muka jin jawabinsa, ya zo jihar ne domin ya ziyarci shugabancin jam’iyyar APC na jihar kuma ya ba da tallafinsa ga jam’iyyar. Wanda shi ne abinda ya fi muhimmanci a wajensa. 
Bayan ya ba da tallafin nasa ne kuma ya juya zai tafi, sai ‘yan jarida suka yi masa caa! Suka takale shi a kan batun tsayawarsa takara don gadar gadon Gwamna Sani Bello a 2023. 

Wannan tambaya ta sa ya koma ya sake ɗaukar abin magana don ba da amsa. Sannan Kaakaki Nupe ya dubi manema labaran ya ce: “Kuna so dai yau na kwance muku bakin jaka ko? Eh, ina da muradin tsayawa takarar gwamnan jihar Neja, amma a yau na zo ne don na kawo ziyara ga wurin da nake so na tallata manufa ta. Amma ban zo don tallata manufar tawa ba. Amma tunda kun tambaya, ina da muradin tsayawa takarar gwamnan jihar Neja”.

Wannan batu nasa ya sa ɗakin taro ƙara rikicewa da ihu da sowar murna da makamantansu. Wasu magoya bayan ma har rausayawa suka yi don farin ciki da nuna gamsuwarsu. Masu sharhi a kan al’amuran siyasa suna ganin ƙaddamar da takarar Malagi ta buɗe wani sabon shafin siyasa a jihar Neja. Kodayake, wannan kyauta da Malagi ya yi ga APC bai yi wa wasu daga ‘yan adawar Malagi daɗi ba. Domin sun tsorata da irin kyauta ta girma da ya yi wa jam’iyyar domin suna tsoron kada hakan ya sa taurauwarsa ta dusashe ta sauran ‘yan takarar a cikin jam’iyya da kuma wajen al’umma. 

Wata majiya ta cikin jam’iyyar APC da ta nemi a sakaya sunanta/sa ya bayyana wa wakilin Blueprint shi ya bayyana haka. Sannan ya ƙara da cewa, Malagi bai hana kowanne ɗan jam’iyya tallafa wa jam’iyya ba. Don haka, a daina hassada a kan wannan halin girma da ya yi wa jam’iyyar. Babbar matsalar a cewar sa, wasu mambobin jam’iyyar ne da ba sa so su amfanawa jam’iyyar sai dai su su ci amfaninta. Hakazalika kuma a cewar sa, Malagi ya nuna cewa shi mutum ne mai son cigaban jam’iyya ne don haka ya cancanci dukkan jinjina da yabo a cewar sa. 

Iyayen jamiyya sun yi amanna:
Daga irin muƙarrabansa da suka yi masa rakiya da irin tarbar da ya samu, ‘yar manuniya tuni ta nuna cewa Malagi ɗan takara ne mai nagarta. Sannan kuma kusan dukkan ƙusosshin jam’iyyar na jihar suna nan kuma bisa ga alama sun yi mubaya’a da nagartaccen ɗan takarar. Kuma zai yi wuya a iya lissafa ɗimbin manyan mutane masu muhimmanci da faɗa a jin da suka rako shi Minna saboda yawansu. Wasu daga ciki sun haɗa da Ambassador Ahmed Musa Ibeto wanda tsohon mataimakin gwamnan jihar Neja ne wanda ya yi ƙoƙari sosai a lokacin da yake kan mulki a 2014. Sannan akwai tsohon sanata mai wakiltar Neja ta Arewa, Sanata  Ibrahim Musa da tsohon Kakain majalisar Neja, Honarabul  Marafa Guni wanda har yau yana majalisar dokokin.  

A yayin zantawarsa da wakilin Blue print, Ibeto ya bayyana Malagi a matsayin Nagartaccen ɗan takara wanda ya riga ya yi rawa tun a baya, kuma an gani. Kuma shi ne  wanda idan har ya samu dama, tabbas zai kawo haɗin kan jam’iyyar ta zama tsintsiya maɗaurinki guda. Donhaka a cewarsa, yana goyon bayan Malagi ɗari bisa ɗari. Domin gudunmowar da ya bayar a yau za ta taimaka wajen ɗinke ɓarakar da ta daɗe a jamiyyar APC a jihar.
 
Kwalliya ta fara biyan kuɗin sabulu:
A yanzu haka dai kwalliya ta fara biyan kuɗin sabulu game da gudunmowar Malagi ga jam’iyyar APC.
Domin farin jinin jam’iyyar APC ya ƙara ninkuwa saboda yawan ganin giftawar motocin da ya bayar masu ɗauke da hatimin jam’iyyar.  APC ce kaɗai take da wannan tagomashin daga cikin jam’iyyun jihar. 

Wani dattijon jam’iyya,  Adamu Idris ya faɗa wa wakilin Blueprint cewa, bayyanar motocin da Malagin ya ba wa jam’iyya ko’ina a titunan garin Minna wata hanya ce ta tallata jam’iyyar da yi mata kamfe gabanin fara kamfe ɗin zaɓen 2023. Don haka ya ce, ya na kira ga sauran mutanen jam’iyyar da su yi koyi da Kakakin Nufe.

Blueprint Newspaper jarida ce, wacce take fitowa a kullum wacce ake wallafa ta a Abuja, Nijeriya  adireshinta na yanar gizo shi ne, https://blueprint.ng. Manhaja ita ce ta Hausarta da za a iya samun ta a https://manhaja.blueprint.ng.