2023: Zaman ɗar-ɗar kan mataimakin da Tinubu ya zaɓa

*Ganduje, Shettima da Masari na neman yin zarra
*Dogara da Lalong na cigaba da tseren
*Atiku ya bayyana dalilinsa na zaɓen Okowa maimakon Wike

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja

A daren jiya Alhamis, kimanin awanni 24 kafin ƙarewar wa’adin da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC) ta bayar na miƙa ’yan takarar mataimakan Shugaban Ƙasa na jam’iyyun Nijeriya, zaman ɗar-ɗar ya ƙaru kan wanda ɗan takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar APC mai mulkin ƙasar, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, zai zaɓa a matsayin wanda zai take masa baya a matsayin ɗan takarar Mataimakin Shugaban Ƙasa sakamakon yanayin yadda lissafin siyasar ƙasar ke cigaba da cuɗawa.

A jiyan dai an jima ana tsumayin sakamakon ganawar da aka yi tsakanin Tinubu da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari akan batun tsayar da mataimakin, inda aka yi tsammanin bayan fitowar Tinubu daga ganawar a Fadar Shugaban Ƙasa zai sanar da wanda zai mara masa bayan.

An tattaro bayanai cewa, kwamitin jam’iyyar ya tantance mutum biyar bayan an shafe kwanaki ana tattaunawa.

Mutanen da suka shiga jerin sunayen sun haɗa da: Tsohon Gwamnan Jihar Borno, wanda kuma shi ne Daraktan Yaƙin Neman Zaven Tinubu, Kashim Shettima; Gwamnan Jihar Filato, Solomon Lalong; tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara; Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje; da Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari.

Bayanai sun nuna cewa, sakamakon tsamarin da aka shiga na kasancewar Tinubu mabiyin addinin Musulunci amma daga yankin Kudancin Nijeriya, wanda hakan ke nuni da cewa, a addinance ya fito daga tsirarun yankinsa kenan, don haka ake ganin cewa, idan ya zavi Kirista daga yankin Arewacin Nijeriya, to tsiraru biyu ne za su yi takara kenan, domin Kiristoci ne tsirarun Arewa.

Wannan ya sanya masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da dama ke ganin dacewar ya runtse idanu ya zaɓi Musulmi daga Arewa, don hakan na nuni da cewa, ba a zaɓi tsiraru daga yankin ba kenan, kamar yadda ya faru a zaɓen Marigayi MKO Abiola a 1991, wanda kuma ake ganin sun samu nasara shi da Babagana Kingive, duk da kasancewarsu Musulmi duka.

Har zuwa lokacin da aka tafi buga Blueprint Manhaja a daren jiya, ba a samu sakamakon fitar da ɗan takarar Mataimakin Shugaban Ƙasa na APC ba, inda jiga-jigan tafiyar da jam’iyyar ke can suna cigaba da ganawa, don fitar da kyakkyawan sakamakon da zai iya yin karo da ɗan takarar babbar jam’iyyar adawa ta PDP, wanda tuni ya bayyana wanda zai yi masa takarar mataimaki.

Shi kuwa ɗan takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya bayyana Gwamnan Jihar Delta, Ifeanyi Okowa, a matsayin wanda zai yi ma sa takarar Mataimaki Shugaban Ƙasa saɓanin Gwamnan Jihar Ribas, Wike, wanda ya zo na biyu a lokacin zaɓen fitar da gwani.

Da ya ke jawabi a wajen ƙaddamar da takarar a sakatariyar jam’iyyar ta ƙasa, Atiku ya bayyana, dole ne abokin takararsa ya zama wanda zai iya aiki da shi, ya amince da shi kuma zai mara masa baya da zuciya zaya domin ya kai ƙasar nan zuwa ga tudun mun tsira.

A cikin jawabin da ya yi a wurin taron, ya ce, “bari in fara da sake yaba wa babbar jam’iyyarmu don shiryawa da kuma kammalawa, za a iya cewa, babban taron ya samar da ni a matsayin mai riƙe da tutarmu a zaɓen shugaban ƙasa na shekara mai zuwa.

“Na sake yaba wa ’yan’uwana masu son yin takara a wannan tafiya. Ina yi musu godiya kan wasan motsi. Sun yi faɗa mai ƙarfi domin suna kula da ƙasarmu. Ni da kaina na zagaya don gode musu tare da neman haɗin kansu don gwagwarmayar da ke gaba.

“Haɗin kan jam’iyyu yana da matuƙar muhimmanci ba kawai a gare mu mu gabatar da yaqin neman zaɓe ba har ma don samar da kyakkyawan shugabanci wanda ƙasarmu ta cancanta da gaske kuma al’ummarmu ke fata. Aikin lashe zaɓuka masu zuwa zai kasance mai wahala kuma kada mu ɗauki wani abu da wasa,” inji Atiku a wajen taron.

Ya ƙara da cewa, “a lokacin da na kai ga yanke shawara, na yi tattaunawa da masu ruwa da tsaki a jam’iyyarmu da suka haɗa da Gwamnoninmu, da kwamitin ayyuka na aasa, da kwamitin amintattu, da sauran shugabanni domin neman shawarwarinsu da hikimarsu.

“A cikin waɗannan shawarwari, na bayyana cewa abokin takarata zai sami damar gaje ni a ɗan lokaci kaɗan, wato, shugaba mai jiran gado.

“Wato dole ne mutum ya kasance yana da halayen da zai zama Shugaban ƙasa. Dole ne mutun ya san irin halin da gwamnatin APC ta jefa ƙasarmu a ciki; ya fahimci irin wahalhalun da akasarin mutanenmu suke ciki da kuma gaggawar kawar musu da wannan wahala; ya fahimci muhimmancin ci gaban tattalin arziki da cigaba don samarwa matasanmu ayyukan yi, cikar buri, da hanyar samun arziki,” inji shi.

Ya ce, “dole ne mutum ya fahimci muhimmancin ilimi a cikin ci gaban al’ummomin zamani don haka za mu iya shirya matasanmu don samun damar yin gasa a duniya da ke daɗaɗa gasa da duniya.

“Dole mataimaki ya fahimci cewa idan ba tsaro ba, cigaba zai yi matuƙar wahala domin masu zuba jari na cikin gida da na waje waɗanda tuni suka tsorata, ba za su koma zuba jari a tattalin arzikinmu ba. Don haka, abokin takarata zai zama mutumin da zai tsaya min yayin da na ke fuskantar matsalar rashin tsaro mai ban tsoro a cikin ƙasarmu.

“Kamar yadda kuka sani gwamnatin APC ta yi barci yayin da ɗimbin yankunan ƙasarmu suka faɗa hannun ‘yan ta’adda na miyagun ayyuka da suka haɗa da masu yin kamfen a matsayin masu fafutukar neman ’yanci ko makiyaya, yayin da manomanmu da makiyaya na gaske suka kasa gudanar da harkokinsu,” inji shi.

Ya ci gaba da cewa, “bugu da ƙari, abokin takarata ya zama wanda ba ya tsoron faɗin ra’ayinsa da bayar da shawarwari na gaskiya, kuma a kasance tare da ni, ina bakin ƙoƙarina wajen ganin an kawar da ɓarnar da aka yi a cikin shekaru bakwai na gwamnatin APC.”

Ya ce, “ina son mataimakina ya kasance tare da ni yayin da na ke aiki tuƙuru a kowace rana don samar wa jama’armu tsaro, farfaɗo da tattalin arzikinmu, inganta ilimi da haɗa kan ƙasarmu. Yana da gogewa na Majalisa da na zartarwa. Da fatan za a yi min maraba da tikitin takarar mataimakin shugaban Tarayyar iajeriya mai girma Gwamna Dakta Ifeanyi Arthur Okowa.