2023: Zan janye aniyata ta neman shugabancin ƙasa idan APC ta miƙa tikiti ga yankin Kudu – Yerima

Daga BASHIR ISAH

Tsohon Gwamnan Zamfara, Ahmed Yerima, ya bayyana cewa zai janye aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2023 muddin jam’iyyar APC ta miƙa tikitin takarar Shugaban Ƙasa ga yankin Kudu.

Yerima ya bayyana haka ne yayin wata ganawa da ya yi da manema labarai a Abuja a Lahadin da ta gabata.

Tsohon sanatan ya ce duk da matsayar da gwamnonin Kudu suka cim ma a wani taronsu da suka yi a Legas, bai ga dalilin da zai sanya shi janyewa daga takarar neman shugabancin ƙasa ba.

Ya ce, “Ina mai tabbatar muku da cewa idan Allah Ya sa ina raye, ni Sanata Ahmed Sani, ina da niyar neman kujerar Shugaban Ƙasa.

“Amma idan gobe jam’iyyata (APC) ta ce ta miƙa damar takarar Shugaban Ƙasa ga yankin Kudu, ni Yarima zan yi biyayya.”

Da yake anmsa tambayar kan ko zai bar APC idan ya zamana APCn ta damƙa wa yankin Kudu tikitin takarar Shugaban Ƙasa, Yerima ya ce ba shi da niyar barin wata jam’iyya zuwa wata.

A cewarsa, “Ni mutum ne mai tsantsenin addini. A matsayina na Musulmi na san cewa Allah Shi ke ba da mulki. Da farko, idan Allah bai ƙaddare ni da zama Shugaban Ƙasa ba, hakan ba zai faru ba. Ban taɓa barin jam’iyyata ba…”

Ya ce shi cikakken ɗan APC ne kuma ba ya tunanin barin ta zuwa wata jam’iyya. Tare da cewa, idan aka bi tsarin karɓa-karɓa aka bai wa Kudu damar shugabancin ƙasa, “Na san lokacina ne ya wuce. Amma na tabbata Allah da kanSa zai yi hukunci amma ba mutane ba,” in ji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *