2024: Kebbi ta karɓi baƙuncin gasar karatun Alƙur’ani ta ƙasa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Jihar Kebbi ta karɓi baƙuncin gasar karatun Alƙur’ani ta ƙasa na tsawon mako guda na shekara ta 2024, wanda aka shirya gudanarwa tsakanin 20 zuwa 28 ga watan Disamba na wannan shekara.

Wani babban kwamitin da ya ƙunshi fitattun malaman fikihu, malamai da ƙwararrun gwamnati a ƙarƙashin jagorancin Sarkin Argungu, Alhaji Sama’ila Muhammadu Mera, ya gudanar da wani taron ƙaddamarwa a fadar sarkin, a ranar Litinin.

Sarkin ya tunatar da ‘yan uwa irin girman aikin da ke gabansu, inda ya yi kira da a jajirce wajen ganin an samu nasara.

“Ina godiya ga Gwamna Nasir Idris da ya naɗa mu don karrama Alƙur’ani mai girma da rukunan addini.

“Muna da babban aiki a gabanmu, muna godiya ga Allah da Ya ba mu damar ciyar da wannan aiki na Musulunci gaba, wanda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi wasicci ga Musulmi.

“Muna addu’ar Allah ya sanya makon karatun ya zama albarka ga Kebbi da Nijeriya baki ɗaya, Allah ya kawar mana da dukkan ƙalubalen da al’ummarmu ke fuskanta,” Sarkin ya yi addu’a.

Ya sanar da ‘yan kwamitin cewa Kebbi za ta karɓi baƙuncin mutane daga sassa daban-daban na ƙasar nan, don haka dole ne su yi aikinsu da tsoron Allah.

“Muna da alhakin kiyaye amana da amanar da shugabanmu Gwamna Nasir Idris ya ba mu; Kada mu ba shi kunya ko ta yaya”, in ji mai martaba Sarkin.

Kwamishinan harkokin addini na jihar Kebbi, Alhaji Muhammad Sani Aliyu, shi ne mataimakin shugaban kwamitin, tare da babban sakatare a harkokin majalisar zartarwa, Dr. Nasir Kigo, a matsayin sakatare.

Sauran membobin sun haɗa da kwamishinonin yaɗa labarai da al’adu; Kiwon Lafiyar Dabbobi; Ilimi Matakin Farko da na Sakandare; Matasa da Ci gaban Wasanni; Harkokin Mata; da kuma Kwamishinan Muhalli.

Haka kuma a cikin kwamatin akwai Shugaban Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Waziri Umaru Federal Polytechnic, Birnin Kebbi, Dr. Usman Sani Tunga, da babban limamin masallacin Birnin Kebbi, Sheikh Mukhtar Walin Gwandu.