2027: Ɗan Majalisar Wakilan Zamfara ya musanta rahoton gargaɗi ga Ganduje da El-Rufai

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Ƙaura Namoda da Birnin Magaji a Jihar Zamfara Hon. Aminu Sani Jaji ya ƙaryata rahoton ɗaya daga cikin kafafen yaɗa labarai na yanar gizo cewa ya gargaɗi Ganduje da El’Rufa’i kan zaɓen 2027, yana mai bayyana rahoton a matsayin wani yunƙuri na wasu ɓatagari da nufin ɓata masa suna a siyasance.

Dr. Aminu Sani Jaji a wata sanarwa da ya fitar ya bayyana cewa bai yi magana da wata kafar yaɗa labarai ba ballantana ya rubuta wata magana mai alaƙa da wannan batu inda ya danganta rahoton a matsayin yunƙurin wasu sheɗanun ‘yan siyasa waɗanda ba su da wani alheri ga jam’iyyar APC mai mulki.

A cewarsa, zai ci gaba da kasancewa mai biyayya ga jam’iyyar APC da jajircewa wajen samun nasarar shugaba Tibubu.

Ya kuma ƙara da cewa irin wannan magana ba za ta fito daga gogaggen ɗan siyasa irinsa wanda ya sadaukar da dukiyarsa da ƙarfinsa da lokacinsa tun farkon kafa jam’iyyar APC a shekarar 2013 zuwa yau ba, kuma zai ci gaba da kasancewa a jam’iyyar ta APC a kowane lokaci.

“Zan ci gaba da kasancewa mai biyayya ga gwamnatin Shugaba Tibubu’ wanda na ɗauka a matsayin jagora sannan kuma ina goyon bayan duk wani mataki da jam’iyyar APC ƙarƙashin jagorancin Abdullahi Umar Ganduje take ɗauka wanda zai taimaka wa Shugaba Tinubu wajen cika alƙawuran yaƙin neman zaɓe da ya yi wa ‘yan Najeriya”. Yace

Dangane da tsohon Gwamna Nasir El-Rufai Hon. Aminu Sani Jaji ya bayyana shi a matsayin babban ɗan siyasa wanda yasa jam’iyyar APC a zuciyarsa duba da ƙoƙarinsa na ganin jam’iyyar ta samu nasara a 2023.

“Zan iya tunawa yadda El’Rufa’i ya yi aiki da wasunmu tun 2013 don ganin jam’iyyar ta samu nasara a 2015, kuma zan iya tunawa da irin gwagwarmayar da ya yi wajen ganin an samu nasarar Shugaba Tibubu a zaɓen fidda gwani na 2023 da kuma a zaɓen gama-gari, kuma ni kaina na yi imani da hakan, duk da cewa akwai wasu ɓangarori na rashin jituwa da El-Rufa’i, amma Insha Allahu za a sasanta.”

Hon. Jaji ya yi kira ga jama’a da su yi watsi da rahoton na jaridar LEGIT, sannan su ci gaba da marawa gwamnatin shugaba Tibubu baya domin ta samu nasara tare da marawa tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje kyakkyawan aiki na tabbatar da nasarar jam’iyyar APC a 2027.

Hon Aminu Sani Jaji ya kuma yi kira ga shugabannin jam’iyyar da suka haɗa da Malam Nasir El-Rufai da su ajiye bambance-bambancen da ke tsakanin su, su ƙara himma wajen ganin jam’iyyar APC ta samu nasara a zaɓen 2027.