Daga AISHA ASAS
Sanannen abu ne cewa, a ‘yan shekarun nan, mawaƙan Nijeriya ne suka amshe kaso mafi rinjaye na waƙoƙin da aka fi ji da tashe a duniya. wannan ne ya sa duniya ba ta da zaɓi face ayyana su a matsayin manyan mawaƙan duniya, wanda hakan ya kawo tazgaro ga manyan mawaƙan Turawa da wasu ƙasashen waɗanda a baya suke a layin farko da ake ji da ganinsu a kodayaushe.
Mawaƙa irin su Rema, Daɓido, Burna Boy da makamantansu sun kasance masu jan zare a waƙoƙin duniya na ɗan tsayin lokaci, wanda hakan ya sanya suke wasan ƙwallon ƙafa da duk wasu kambun karramawa, ko sanannun bukukwan karrama mawaƙa da makamantansu.
An jima ana jin su a layin farko a tarukan karramawa na duniya, wanda ya ba wa Nijeriya ƙima da suna a tsakanin ƙasashen da ke ganin sun fita.
Saidai a wannan shekarar za mu iya cewa, ta canza zane, amma fa ga mawaƙan, ba ga ƙasar Nijeriya ba. Grammys ɗaya daga cikin taruka masu matuƙar muhimmanci ga mawaƙa da duk wasu da suka jiɓinci sana’ar nishaɗantarwa. Kuma yana ɗaya daga cikin tarukan da mawaƙan Nijeriya ke darawa, da kuma tabbatar da sun iya, sakamakon zaɓarsu da ake yi sama da kaso mai yawa na takwarorinsu na wasu ƙasashen.
A wannan shekarar kamar yadda muka ce, mawaƙan ne ta canzawa ba ƙasar da suka fito ba, kasancewar manyan mawaƙan Nijeriya da suka saba haskawa a wannan taron sun disashe, yayin da sabuwar fuska ita ma daga Nijeriya ta maye gurbinsu, wato Tems.
An gudanar da bikin karramawar Grammy na 2025 a ranar Lahadi, 2 ga Fabrairu, inda aka yi bikin babbar dare na kiɗa tare da Tems ta Najeriya cikin waɗanda suka yi nasara a daren.
Tems ta ci lambar yabo a matsayin mafi kyawun bidiyon waƙa a Afirka a rukunin da mawaƙan Najeriya suka mamaye, ciki har da Burna Boy da Asake.
Mawaƙiyar ta samu wannan nasara ce da waƙarta mai suna ‘Loɓe Me Jeje’ daga kundinta na farko mai suna ‘Born in the Wild’ wanda hakan ya sa ta zama ta biyu a tarihin wannan rukuni, wanda aka haifa a shekarar da ta gabata kuma ɗan Afirka ta Kudu Tyla ta fara lashewa.
“Ya Ubangiji, na gode sosai da ka sanya ni a wannan mataki da ka kawo ni a wannan tawaga,” inji Tems a jawabinta a yayin karɓar karramawar. Sannan ta sadaukar da kyautar ga mahaifiyarta, wacce za ta yi bikin ranar haihuwarta a kashe garin taron wato, a ranar 3 ga Fabrairu.