Zaɓen gwamnoni: Sufeto-Janar ya ba da umarnin taƙaita zirga-zirga

Daga BASHIR ISAH

Yayin da zaɓen gwamnoni da na majalisun jihohi ya kawo jiki, Sufeto-Janar na ‘Yan Sandan Nijeriya, Usman Baba, ya ba da umarnin taƙaita zirga-zirgar abubuwan hawa a kan tudu da ruwa da dangoginsu a ranar zaɓe.

Wannan umarni zai fara aiki ne daga ƙarfe 12 na tsakar dare zuwa 6 na yamma na ranar zaɓen.

Sai dai umarnin ya sahale wa jami’an INEC da masu sanya ido da ‘yan jaridar da aka tantance da makamantansu damar zirga-zirga a wannan rana ta zaɓen.

“Wannan umarni bai shafi yankin Abuja ba sakamakon babu wani zaɓe da za a gudanar a yankin a wannan rana,” kamar yadda Kakakin rundunar, Muyiwa Adejobi, ya bayyana.

“Kazalika IGP ya jaddada haramcin dogarai su yi wa ubannin gidansu da ‘yan siyasa rakiya zuwa rumfunan zaɓe yayin zaɓen,” in ji shi.

Haka nan, ya haramta harkokin tsaron jihohi da na masu zaman kansu, irin su Benue State Community Volunteer Guards da Amotekun Corps da Ebubeagu da dai sauransu, daga shiga hakokin zaɓen.

Daga nan, IGP ya buƙaci ‘yan ƙasa da su kasance masu kiyaye doka da oda yayin da kuma bayan zaɓen, tare da ba da tabbacin an cimma dukkan tsarin da ya kamata domin tabbatar da tsaro a faɗin ƙasar a lokacin zaɓe.