Aƙalla ‘yan Nijeriya miliyan 90 ne za su kaɗa ƙuri’a a zaɓen 2023 – INEC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar Zaɓe Mai zaman Kanta ta Ƙasa, INEC ta ce tana kyautata zaton aƙalla ‘yan Nijeriya miliyan 90 za su kaɗa ƙuri’a a babban zaɓen ƙasa mai zuwa na 2023.

Shugaban hukumar Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka yayin da ya kai ziyara ofishin hafsan sojin saman Nijeriya IO Amao a Abuja babban birnin ƙasar.

Shugaban hukumar zaɓen ya nemi taimakon rundunar sojan saman Nijeriya wajen ganin an isar da kayan zaɓe a ƙananan hukumomi a lokaci guda lokacin zaɓe.

Yakubu ya ce aiki da rundunar shine mafita wajen kare yiwuwar samun tsaiko wajen isar da kayayyakin zaɓe musamman a yayin da hukumar ke ƙoƙarin ganin ta yi zaɓen gwamna a jihar Ekiti aƙalla nan da makwanni biyu masu zuwa.

Ya jaddada muhimmancin kai kayayyakin zaɓe a runfunan zaɓe 190,000 lokacin zaɓen ‘yan majalisu a duk faɗin ƙasar, wanda ake buƙatar ganin an yi zaɓe a lokaci guda wato daga ƙarfe 8:30 na safe zuwa 2:30 na yamma.

Yayin jawabinsa hafsan sojin saman Nijeriya, Amao ya ce rundunar a shirye take don ganin ta taimakawa hukumar ta INEC wajen gudanar da ayyukan zaɓe ba tare da wata matsala ba.