A ƙarshe, APC ta miƙa kujerar shugaban jam’iyya ga Arewa-ta-tsakiya

*Ta amince da tsarin karɓa-kaarɓa

Daga BASHIR ISAH

Yayin da lokacin babban taronta na ƙasa ke daɗa ƙaratowa, jam’iyyar APC ta miƙa kujerar shugabancin jam’iyya ga shiyyar Arewa-ta-tsakiya, sannan kujerar Sakataren Jam’iyya na Ƙasa ga shiyyar Kudu-maso-yamma.

Sanarwar da Daraktan Yaɗa Labarai na Jam’iyyar, Salihu Na’inna Ɗambatta ya fitar ta nuna shiyyar Kudu-maso-gabas ne zai samar da mataimakin shugaban jam’iyya na ƙasa, yayin da shiyyar Kudu-maso-kudu za ta samar da sakataren yaɗa labarai na ƙasa da sauransu.

A halin da ake ciki dai Kwamitin riƙo da shirya babban taron APC (CECPC) ya amince da tsarin karɓa-karɓa dangane da babban taron jam’iyya. Kwamitin ya cimma wannan matsaya ne yayin zaman da ya yi a ranar 8 ga Maris, 2022.

Ga cikakken bayani kan yadda tsarin yake:

AREWA-TA-TSAKIYA:
Mai ƙunshe da jihohin Binuwai, Kogi, Kwara, Nasarawa, Niger da kuma jihar Filato.

 1. Shugaban Jam’iyya na Ƙasa (Arewa-ta-tsakiya)
 2. Mataimakin Shugaban Jam’iyya
 3. Mataimakin Sakatare na Ƙasa
 4. Mataimakin Mai bada Shawara Kan Sha’anin Shari’a
 5. Mataimakin Sakataren Yaɗa Labarai
 6. Sakataren Shiyya
 7. Shugaban Matasa na Shiyya
 8. Sakataren Tsare-tsare na Shiyya
 9. Shugabar Mata ta Shiyya
 10. Shugaban Masu Fama da Nakasa na Shiyya
 11. Tsohon Jami’i na Ƙasa

KUDU-MASO-KUDU:
Mai ƙunshe da jihohin;l Akwa Ibom, Bayelsa, Cross River, Delta, Edo da kuma Rivers.

 1. Mataimakin Shugaban Jam’iyya (Kudu-maso-kudu)
 2. Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa
 3. Shugabar Mata ta Ƙasa
 4. Mataimakin Ma’aji ns Ƙasa
 5. Mataimakin Sakataren Walwala na Ƙasa
 6. Sakataren Shiyya
 7. Shugaban Matasa na Shiyya
 8. Sakataren Tsare-tsare na Shiyya
 9. Shigabar Mata ta Shiyya
 10. Shugaba na Musamman na Shiyya (ga masu fama da nakasa)
 11. Tsojon Jami’i na Ƙasa

KUDU-MASO-YAMMA:
Mai ƙunshe da jihohin Ekiti, Lagos, Ogun, Ondo, Osun da kuma Oyo.

 1. Sakatare na Ƙasa
 2. Mataimakin Shugaban Jam’iyya na Ƙasa (Kudu-maso-yamma)
 3. Shugaban Matasa na Ƙasa
 4. Shugaban Masu Fama da Nakasa na Ƙasa
 5. Mataimakin Odito na Ƙasa
 6. Sakataren Shiyya
 7. Shugaban Matasa na Shiyya
 8. Sakataren Tsare-tsare na Shiyya
 9. Shugabar Mata ta Shiyya
 10. Shugaban Masu Fama da Nakasa na Shiyya
 11. Tsohon Jami’i na Ƙasa

KUDU-MASO-GABAS:
Mai ƙunshe da jihohin Abia, Anambra, Ebonyi, Enugu da kuma Imo.

 1. Mataimakin Shugaba na Ƙasa (Kudu)
 2. Mataimakin Shugaba na Ƙasa (Kudu-maso-gabas)
 3. Ma’aji na Ƙasa
 4. Sakataren Walwala na Ƙasa
 5. Mataimakin Sakataren Tsare-tsare na Ƙasa
 6. Sakataren Shiyya
 7. Shugaban Matasa na Shiyya
 8. Sakataren Shiyya
 9. Shugabar Mata ta Shiyya
 10. Shugaban Masu Fama da Nakasa na Shiyya
 11. Tsohon Jami’i na Ƙasa

AREWA-MASO-GABAS:
Mai ƙunshe da jihohin Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Taraba da kuma Yobe.

 1. Mataimakin Shugaba na Ƙasa (Arewa)
 2. Odito na Ƙasa
 3. Mataimakin Shugaba na Ƙasa (Arewa-maso-gabas)
 4. Mataimakin Sakataren Kuɗi
 5. Mataimakiyar Shugabar Mata ta Ƙasa
 6. Sakataren Shiyya
 7. Shugaban Matasa na Shiyya
 8. Sakataren Tsare-tsare na Shiyya
 9. Shugabar Mata ta Shiyya
 10. Shugaban Masu Fama da Nakasa na Shiyya
 11. Tsohon Jami’i na Ƙasa

AREWA-MASO-YAMMA:
Mai ƙunshe da jihohin Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Sokoto da kuma Zamfara.

 1. Mataimakin Shugaba na Ƙasa (Arewa-maso-yamma)
 2. Mai Bada Shawara Kan Sha’anin Shari’a na Ƙasa
 3. Sakataren Tsare-tsare na Ƙasa
 4. Sakataren Kuɗi na Ƙasa
 5. Mataimakin Shugaban Matasa na Ƙasa
 6. Sakataren Shiyya
 7. Sakataren Matasa na Shiyya
 8. Sakataren Tsare-tsare na Shiyya
 9. Shugabar Mata ta Shiyya
 10. Shugaban Masu Fama da Nakasa na Shiyya
 11. Tsohon Jami’i na Ƙasa

Sanarwa ta ce wakilan shiyyoyi na CECPC su ne za su saka ido kan yadda lamurra ke gudana a kowace shiyya.