A ɗaga wa Fulani makiyaya ƙafa kan wa’adin sauya kuɗi – Miyetti-Allah

Daga MAHDI M. MIHAMMAD

Ƙungiyar Kare Muradun Fulani makiyaya ta Miyetti-Allah Kautal Hore ta buƙaci tsari na musamman ga al’ummarta kan wa’adin sauya takardun kuɗi na Naira da aka sanar da wa’adin sauyawa.

Jagoran ƙungiyar Alhaji Abdullahi Bello Bodejo wanda ya bayyana buƙatar a yayin taron ’yan jarida a Abuja a ranar Litinin, ya ce, duk da kwamitoci da ƙungiyar ta kafa don wayarwa jama’arta kan lamarin, ya ce a al’umarsu za ta iya faɗawa matsalar ’yan damfara idan ba a yi mata tanadi na musamman ba.

“Bafulatani ne zai sayar da shanu kamar talatin, amma sai ya ce sai dai a biya shi da ruwan kuɗi kasancewar shi kansa a haka zai biya wasu kuɗin dabbobin tun a kasuwar, sannan idan da ragowar kuɗi ya sa a leda ya wuce da su ruga da ke cikin daji inda babu banki babu layin sadarwa,” inji shi.

Shugaban na Miyetti ya ce, ƙungiyarsu na goyon bayan tsarin sauya kuɗin matuƙar zai taimaka a kan inganta tattalin arzikin ƙasa.

“Buqatar da muke da ita ita ce a ƙara wa’adin zuwa kamar aƙalla wata 6. Ƙasashe irin Saudiyya sun sauya kuɗi a lokuta daban-daban, amma har yanzu suna amfani da kuɗaɗen kamar yadda mahajjata da su kan lamarin suke gani.

“Bayan samun labarin sauya kuɗin mun kafa kwamitocin wayar da kai a kan lamarin, kuma mu na fata a ɓangarenta ita gwamnati za ta duba yiwuyar ƙara wa’adin lokaci da kuma yi wa Fulani makiya da sauran mazauna wurare irin nasu, tanadi na musamman a kai”, inji shi.

Ƙungiyar wadda ta yi taron shugabanninta na jihohi a ranar ta kuma yi zargin kashe jama’arta musamman a jihohin Taraba da Benuwei.

Ya ce, a Jihar Benuwei kuma ana fakewa ne da dokar hana kiwo ana musgunawa makiyaya wasu a tsare su wasu a kashe, sannan a yi gwanjon dabbobinsu, kamar yadda ƙungiyar ta yi zargi.

Ƙungiyar ta Miyetti Allah ta buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta ƙirƙiro ma’aikata ta musamman don kula da sha’anin makiyaya da zai haɗa da kiwo da kuma karantarwa, sannan ta farfaɗo da wuraren kiwo a matsayin hanyar magance masu matsaloli da suke fama da su.