*Ta amince da tsarin karɓa-kaarɓa
Daga BASHIR ISAH
Yayin da lokacin babban taronta na ƙasa ke daɗa ƙaratowa, jam’iyyar APC ta miƙa kujerar shugabancin jam’iyya ga shiyyar Arewa-ta-tsakiya, sannan kujerar Sakataren Jam’iyya na Ƙasa ga shiyyar Kudu-maso-yamma.
Sanarwar da Daraktan Yaɗa Labarai na Jam’iyyar, Salihu Na’inna Ɗambatta ya fitar ta nuna shiyyar Kudu-maso-gabas ne zai samar da mataimakin shugaban jam’iyya na ƙasa, yayin da shiyyar Kudu-maso-kudu za ta samar da sakataren yaɗa labarai na ƙasa da sauransu.
A halin da ake ciki dai Kwamitin riƙo da shirya babban taron APC (CECPC) ya amince da tsarin karɓa-karɓa dangane da babban taron jam’iyya. Kwamitin ya cimma wannan matsaya ne yayin zaman da ya yi a ranar 8 ga Maris, 2022.
Ga cikakken bayani kan yadda tsarin yake:
AREWA-TA-TSAKIYA:
Mai ƙunshe da jihohin Binuwai, Kogi, Kwara, Nasarawa, Niger da kuma jihar Filato.
- Shugaban Jam’iyya na Ƙasa (Arewa-ta-tsakiya)
- Mataimakin Shugaban Jam’iyya
- Mataimakin Sakatare na Ƙasa
- Mataimakin Mai bada Shawara Kan Sha’anin Shari’a
- Mataimakin Sakataren Yaɗa Labarai
- Sakataren Shiyya
- Shugaban Matasa na Shiyya
- Sakataren Tsare-tsare na Shiyya
- Shugabar Mata ta Shiyya
- Shugaban Masu Fama da Nakasa na Shiyya
- Tsohon Jami’i na Ƙasa
KUDU-MASO-KUDU:
Mai ƙunshe da jihohin;l Akwa Ibom, Bayelsa, Cross River, Delta, Edo da kuma Rivers.
- Mataimakin Shugaban Jam’iyya (Kudu-maso-kudu)
- Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa
- Shugabar Mata ta Ƙasa
- Mataimakin Ma’aji ns Ƙasa
- Mataimakin Sakataren Walwala na Ƙasa
- Sakataren Shiyya
- Shugaban Matasa na Shiyya
- Sakataren Tsare-tsare na Shiyya
- Shigabar Mata ta Shiyya
- Shugaba na Musamman na Shiyya (ga masu fama da nakasa)
- Tsojon Jami’i na Ƙasa
KUDU-MASO-YAMMA:
Mai ƙunshe da jihohin Ekiti, Lagos, Ogun, Ondo, Osun da kuma Oyo.
- Sakatare na Ƙasa
- Mataimakin Shugaban Jam’iyya na Ƙasa (Kudu-maso-yamma)
- Shugaban Matasa na Ƙasa
- Shugaban Masu Fama da Nakasa na Ƙasa
- Mataimakin Odito na Ƙasa
- Sakataren Shiyya
- Shugaban Matasa na Shiyya
- Sakataren Tsare-tsare na Shiyya
- Shugabar Mata ta Shiyya
- Shugaban Masu Fama da Nakasa na Shiyya
- Tsohon Jami’i na Ƙasa
KUDU-MASO-GABAS:
Mai ƙunshe da jihohin Abia, Anambra, Ebonyi, Enugu da kuma Imo.
- Mataimakin Shugaba na Ƙasa (Kudu)
- Mataimakin Shugaba na Ƙasa (Kudu-maso-gabas)
- Ma’aji na Ƙasa
- Sakataren Walwala na Ƙasa
- Mataimakin Sakataren Tsare-tsare na Ƙasa
- Sakataren Shiyya
- Shugaban Matasa na Shiyya
- Sakataren Shiyya
- Shugabar Mata ta Shiyya
- Shugaban Masu Fama da Nakasa na Shiyya
- Tsohon Jami’i na Ƙasa
AREWA-MASO-GABAS:
Mai ƙunshe da jihohin Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Taraba da kuma Yobe.
- Mataimakin Shugaba na Ƙasa (Arewa)
- Odito na Ƙasa
- Mataimakin Shugaba na Ƙasa (Arewa-maso-gabas)
- Mataimakin Sakataren Kuɗi
- Mataimakiyar Shugabar Mata ta Ƙasa
- Sakataren Shiyya
- Shugaban Matasa na Shiyya
- Sakataren Tsare-tsare na Shiyya
- Shugabar Mata ta Shiyya
- Shugaban Masu Fama da Nakasa na Shiyya
- Tsohon Jami’i na Ƙasa
AREWA-MASO-YAMMA:
Mai ƙunshe da jihohin Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Sokoto da kuma Zamfara.
- Mataimakin Shugaba na Ƙasa (Arewa-maso-yamma)
- Mai Bada Shawara Kan Sha’anin Shari’a na Ƙasa
- Sakataren Tsare-tsare na Ƙasa
- Sakataren Kuɗi na Ƙasa
- Mataimakin Shugaban Matasa na Ƙasa
- Sakataren Shiyya
- Sakataren Matasa na Shiyya
- Sakataren Tsare-tsare na Shiyya
- Shugabar Mata ta Shiyya
- Shugaban Masu Fama da Nakasa na Shiyya
- Tsohon Jami’i na Ƙasa
Sanarwa ta ce wakilan shiyyoyi na CECPC su ne za su saka ido kan yadda lamurra ke gudana a kowace shiyya.