A ceto fasinjojin jirgin ƙasan Abuja-Kaduna!

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Ni dai duk waɗanda su ka yi min magana bayan kallon faifan bidiyon da ’yan ta’addan da su ka sace fasinjojin jirgin ƙasa kan hanyar Abuja zuwa Kaduna su ka fitar, sun nuna juyayi da kaduwa kana bun da su ka gani. Cin zarafin da ’yan ta’addan su ke yi wa fasinjojin ko ma za a ce farafagandar batawa gwamnati rai ce, amma da ban takaici ainun. Mutane masu ’yanci waɗanda laifin su kaɗai shi ne sun shiga jirgin ƙasa su na nufin sauka a tashar Rigasa da ke Kaduna amma wasu su ka kai mu su farmaki, su ka hallaka wasu inda su ka sace wasu daga cikin su.

Abun da ya qara fitowa fili shi ne waɗanda su ka sace fasinjojin nan ba ’yan bindigar daji da a ka sani ba ne tun farko da ke sace mutane a jihar Zamfara. Waɗannan ɓarayin sun fito da tsari da ya nuna wasu ƙungiyoyi su ka shigo harkar don sauya salon ta’addancin da su ke yi daga mamaye ƙauyuka zuwa amfani da kama mutane don yin musaya da wasu mutanen su da ke gidajen yari.

Ɗaya daga cikin mutanen da su ka yi magana a faifan bidiyon ya yi ikirarin ya na daya daga cikin waɗanda su ka arce daga gidan yarin Kuje. Kazalika ya nuna tamkar satar mutanen aikin Allah su ke yi. Duk da dai Musulunci bai amince a sace mutane ko a ɗauke su haka kawai don cimma wata buƙata ba, amma ba sabon abu ba ne a ga wasu mutane da tambarin Islama su na aikata wani aikin da Islama ya haramta.

Ta’addanci ya daɗe a doron ƙasa ko in ma kawo misalign tun zamanin ’ya’yan Annabi Adamu wato Habila da Ƙabila. In ka ga mutum ya na zalunci yanzu to akwai waɗanda su ka gabace shi da irin wannan mugun aikin kuma akasarin su ba su gama lafiya ba. A je ma wasu an ga sun rayu har su ka mutu a kan gado, amma ai dole dai mutuwar ta ɗauke su.

Illar sace mutane ba ta tsayawa ga abun da wasu ɓarayin kan ce su na aikata haka ne don ɓatawa gwamnati rai, bas a lura ko la’akarai da ’yan uwan waɗanda su ka sacen. Jefa mutane cikin zullumi kasancewar ’yan uwan su na cikin daji babban abun damuwa ne. Duk rashin imanin ɓarawo ai jinin da ya ke yawo a jikinsa ba dabam ba ne da na sauran mutane.

Hakanan ɓarawo ba daga sama ya faɗo ba. Idan ɓarawo ya ce don an kama wani na sa ne ko an ma sa wani zalunci, to haƙiƙa in ya bincika zai samu wanda a ka zalunta fiye da shi kuma ya haƙura bai dau makamai ya na kashe waɗanda ba su yi ma sa laifin komai ba.

Idan ma wanda ke cewa don an ma sa zalunci ne ya sa ya dau makami har da bulala ya na dukan mutane, to ina daidaito a matakin tun da ba wanda ya yi ma sa zalunci ya tava ba, haka kawai hanya yah au ya tare mutane da bai ma san su ba ya tsorita su da barazanar kisa har ma ya gwada cewa ba da wasa ya ke ba kan ɗaya daga mutanen; ai kuwa duk abun da ya samu daga wannan mugun aikin ba wata riba ba ce da za ta yi albarka ko taimaka ma sa a rayuwar duniya ma bare a je lahira.

A gefe guda za a yi sa ran matakan da gwamnati ta ke cewa ta na ɗauka za su yi tasiri wajen ceto mutanen da su ka shafe watanni a dokar daji. A duk lokacin da a ka samu irin wannan takala za ka ji gwamnati na cewa za ta yi dirar mikiya kan ’yan ta’adda.

Wannan karo gwamnati ta fi maida hankali kan zayyana faifan bidiyon da cewa farfaganda ce kuma gwamnati ba za ta raurawa ba a kai. Wato in ma ’yan ta’addan na ɗaukar yadda su ka nuna faifan zai sa gwamnati ta biya mu su buƙata, to sun yi kuskure, don gwamnati za ta ɗauki matakan karɓo mutanen cikin dabaru da jami’an tsaro ke da su da ba za a bayyanawa jama’a ba don hakan zai iya ba wa ’yan ta’addan satar amsa. Mu na fata Allah zai ba da iko a samu karɓo mutanen nan lami lafiya.

Gaskiya amfani da fasahar zamani ma za ta taimaka wajen gano ainihin inda mutanen nan su ke. Ba na son zurfafawa amma ba zan yi mamaki ba in jami’an tsaro ko na sirri sun san inda mutanen nan su ke. Wani abu ma da ya fito da hakan a fili shi ne ba wai gwamnati ba ta son biyewa masu son a yi ruwan wuta don kashe duk miyagun irin ba ne.

Hakanan gwamnatin ta ƙara da cewa in ta aikata haka zuciyar mutane za ta yi sanyi, sai dai abun kula a nan hakan kuma zai shafi waɗanda a ka sacen. Don haka wannan ya na nuna gwamnati na nufin ba ta son yin aikin baban giwa ne garin gyaran gira a tsole idanu. Abun da masu sharhi ke jan hankalin gwamnati shi ne matuƙar akwai wata dabara ya dace a gan ta a tsawon lokacin nan ta yi tasiri.

Zuwa yanzu duk waɗanda su ka fito daga dajin nan, na fitowa ne daga qoqarin danginsu da wa imma kan biya kuɗin fansa ko wata hanyar roƙon alfarma. An samu wasu ko ɗaya daga matan da miyagunsu ka sake don raɗin kansu duk da ba za a ce wai don sun ji tausayin ta ba ne, don kuwa mai tausayi tun farko ba zai sace mutane masu ’yanci ya shige da su daji ba.

Lissafi dai ya nuna zuwa lokacin da na ke rubutun nan akwai sauran mutum 39 a hannun ɓarayin. Cikin fasinjojin akwai maza da mata da ke cikin matuƙar tashin hankali da gajiya da wannan ibtila’a da su ka shiga. Kuma saboda yadda satar ta shafi jirgin ƙasa a karo na farko, hakan ya sa an rage magana kan sauran mutane da a ka sace a sassa daban-daban na musamman Arewa maso yammacin Nijeriya.

Yadda bin hanyar Abuja zuwa Kaduna ya zama abun fargaba kansa a riƙa mamakin duk wanda ya taso daga garuruwan biyu ya iso lafiya. Na samu shaida daga wasu da su ka bi hanyar a dan tsakanin nan na cewa sun ga jami’an tsaro na sintiri don kare jama’ar da ke zirga-zirga kan babbar hanyar da ta zama tamkar babbar ƙofar shiga jihohin arewa maso yamma.

Duk mai bin hanyar wacce tagwaye ce daga Abuja zuwa Kano zai iya ba da shaidar cewa kullum a cike ta ke da motoci da ke kai kawo da jama’a. Motoci kan tsaya a wani bigire in Allah ya sa sun samu labari a kan lokaci kafin su faɗa tarkon ɓarayin. Akwai lokacin da varayin su ka taɓa fitowa ba da niyyar sace jama’a ba sai kawai don su zubar da jinin matafiya haka kawai ba tare da haƙƙin shari’a ba.

Shugaban majalisar amintattu na gamayyar ƙungiyoyin arewacin Nijeriya Nastura Ashir Shariff ya ce taɓarɓarewar tsaro ta kai ga matakin da mutane za su iya ɗaukar matakan kare kansu daga hare-haren miyagun iri.

Nastura Sharif na magana ne kan taɓarɓarewar tsaro musamman bisa fitowar faifan bidiyon fasinjojin jirgin ƙasa da a ka sace kuma miyagu ke azabtar da su ta hanyar duka da bulala.

Hakanan Nastura ya nuna fargabar cewa hatta waɗanda ke cikin babban birnin Nijeriya Abuja ba su tsira daga yiwuwar sacewa ba don ya ce akwai miyagun a yankunan da ke zagaye da birnin.

Shariff ya ce, ba bayanan yawan kuɗin da gwamnati ta kashe kan tsaro ne babban abun dubawa ba, amma irin aikin da a ka yi da kuɗin.

Ɗan gwagwarmayar wanda a ka taɓa tsarewa a hannun ‘yan sanda don niyyar shirya wata zanga-zanga, ya fito ƙarara ya na nuna gwamnati ta gaza.

Hare-hare kan sojoji a yankunan da ba a saba ganin haka ba a baya na sauya tunanin mutane da dama kan yadda ’yan ta’adda ke cin karen su ba babbaka.

Kammalawa:

Ba wani cigaba mai ma’ana da za a samu a ƙasa matuƙar ba tsaron rayuka da dukiyoyon al’umma. Idan har mutane ba za su iya fita daga gidajen su ba su yi tafiya cikin aminci su sauka lafiya ba to akwai gagarumar damuwa. Sufuri na ɗaya daga hanyoyin da ko a can tarihi na taimakawa tattalin arziki ta hanyar samar da kuɗin shiga ga jama’a. Fatake na tafiya daga wannan gari zuwa wancan ko ma a ce daga wannan ƙasa zuwa waccar don sayar da hajarsu, sannan su sayo wata haja da mutanen su ke buƙata su dawo gida.

Da zarar an samu cikas kan hanyar da fataken ke bi hakan zai shafi cinikaiya. Don haka ya na da matuƙar muhimmanci ga gwamnati a dukkan matakai ta yi tsayin daka wajen kare wannan ɓangare na rayuwar jama’a. Har dai mutane na fargabar yin tafiya daga nan zuwa can don neman hanyar kuɗin shiga, ba cigaba mai ma’ana da za a cimma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *