A daina cin zarafin ‘ya’yan riƙo da masu aikatau

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Akwai wata matsala da ta daɗe tana damu na a rai da ta shafi game da yadda wasu mutane ke ɗaukar ‘ya’yan da ba nasu ba cikin su ba, a wulakance, musamman ma dai ‘ya’yan riƙo da suke ɗauko su daga ƙauye ko gidajen ‘yan uwa, don su taimaka musu, ko kuma marayu ne da iyayen su suka rasu. Akwai kuma batun yaran aiki da ake ɗauko su daga ƙauye ko daga gaban iyayen su, don su yi aiki a gidajen masu kuɗi ko ma’aikata, don su taya su aikin kula da gida da yara, a lokacin da masu gida ba sa nan.

Na san kai ma mai karatu ba za ka kasa jin wani labari mai kama da haka, inda wani babban ma’aikaci ko mai kuɗi ya ɗauki wani ko wata daga cikin dangi, ko wata bare da ke masa aiki a gida, amma kuma zamantakewar ta zama mai tsami, babu kulawa ko jin daɗi. Ta iya yiwuwa kai ma ko ke ma, ka taɓa zama ƙarƙashin kulawar wani ɗan uwa, amma ba ka ji daɗin zaman ba. Ko da yake a wani bangaren za ka ga ta ɓangaren maigidan ba ka da wata damuwa da shi, amma daga wajen matan gidan rayuwar sai a hankali. Babu tausayawa babu mutuntawa. Suna mantawa da cewa su ma yaran da ake ba su riƙo da ‘yan aikinsu, su ma ’ya’ya ne, uwa ce ta haife su kamar kowanne ɗa, kuma suna da ’yanci a ƙarƙashin doka, ba bayi ba ne!

Na sani ba duka aka taru aka zama ɗaya ba, akwai mutanen da suke ɗaukar yaran da ba nasu ba su riƙe tare da yaran cikin su har ka kasa bambanta wanne ne ainihin yaran gidan, ana kula da haƙƙin kowa, kuma ana ba su tarbiyyar da ta dace. Ko da ‘yan aiki suka ɗauka za ka ga suna tattalinsu, har ma su saka su a makaranta, kuma suna biyansu haƙƙoƙin su a kan lokaci. Sai dai ba su ne akasari suka fi yawa a cikin al’umma ba, don dama ba a taru an zama ɗaya ba.

Sai dai rubutuna na yau a kan waɗancan mugayen masu zaluntar yaran ’yan uwansu ko yaran aikinsu, ba tare da tausayawa ko tunanin abin da suke yi bai dace ba. Wasu kar ma a je da nisa, ana maganar yaran ‘yan uwa daga ƙauye ko gidajen ‘yan uwa, akwai masu zaluntar ‘ya’yan kishiyoyi da aka mutu ko uwar ta fita ta barsu a tsakar gida, wulaƙanci iri-iri da tozartawa babu wanda ba a nuna musu. Duk dai don ta tabbatar musu cewa su ba ‘yan gata ba ne ko kuma ba ‘yan gida ne.

Masu irin wannan halin, suna nuna wa ‘ya’yansu na cikin su kulawa da soyayya matuƙa, har ma ba sa ganin laifin su a inda suka yi ba daidai ba, a kan masu yi musu aiki ko sauran yaran gida da ba a gidan aka haife su ba. Wani lokaci ma yaran gida kan yi wa ’yar aiki fyaɗe ko wani nau’i ba cin zarafi, amma sai a ɓoye a tsorata yarinyar da uwar ta don kar a fallasa. Kai har ma da zargin ’yar aikin ko ’yar riƙon kan ita ce ta ƙulla makircin.

Kwanakin baya wani abin takaici ya faru da wata yarinya ’yar shekaru goma sha ɗaya da aka rabo ta daga gaban iyayen ta tun daga Jihar Kebbi zuwa Jos, don ta yi wa wata ma’aikaciya da ke aiki a wata babbar ma’aikata, aikin kula da gida, amma sai ta riƙa ƙuntata mata, duka da mugunta, har da zaunar da ita a tafasasshen ruwan zafi, ko da yake daga bisani mijin matar ya ce faɗuwa ta yi a cikin ruwan zafin. Amma sakamakon haka yarinyar ta shiga wani mawuyacin hali, har ma kuma kawo lokacin haɗa wannan rubutun ta rasa ranta. Ita kuma matar tana tsare a wajen hukuma.

Wasu matan sam ba su iya kula da ɗan wani ba. Suna ganin kamar ‘ya’yansu ne kawai abin nunawa so da ƙauna. Sauran yara kuma banza. Haka wani lokaci a can baya aka rawaito cewa, wata mata a Jihar Adamawa ta ƙona jikin wata ƙaramar yarinya da ta ke yi wa aiki, ta hanyar manna mata dutsen guga a jiki. Don kawai ta yi kuskure ga wajen wani aiki da aka ba ta. Wannan wacce irin mugunta ce haka da mata suke nunawa yara mata ƙanana da ke taimaka musu a gida.

Ƙorafe-ƙorafe na yawa game da yadda mata ke wulaƙanta ‘ya’yan wasu da aka ba su amanar riƙewa, ko ma suka je suka rage murya a ba su don su taimaka musu. Amma kafin a je ko’ina sai a fara ganin yarinya ta fara shiga wani yanayi, saboda mugun hali da uwar riƙon ta ke nuna mata. Babu abinci a wadace, babu sutura mai kyau, babu karatu, babu kulawar lafiya ko wata lalura ta ’ya mace, haka ake barin wasu yaran cikin ƙazanta da rashin kula. Su ne wanke wanke, su ne shara da goge-goge, wankin bayan gida, zuwa cefane, girki, da riƙon yara, amma babu kyakkyawar kulawa. Wasu ma ko kwabo ba a biyansu. An ɗauko su ne kawai don su yi rayuwar bauta a gidan wasu, ba tare da wata kula da tarbiyyar da za ta mayar da su mutane nagari ba.

An hana wa waɗannan yara yin rayuwa kamar sauran yara, babu wasannin ƙuruciya, ko shiga cikin sauran yara, sai tsawa da hantara. A irin gidajen da ake sa ’yan aiki a makaranta ma, ba a yarda a sa su a makaranta iri ɗaya da ta sauran yaran gida, kuma ba sa tafiya sai sauran yaran gida sun shirya tsaf an kai su tasu makarantar, su kuma sai su taka da ƙafa su tafi, inda aka sa su.

Wannan mugun hali da mata suke nuna wa yana tauye wa yarinya haƙƙinta, walwalar ta da rayuwarta, kuma suna gadarwa ‘ya’yansu wata irin rayuwa da ba su san yadda za ta kasance da su ba. Su ma wani dalili ya yi sanadin shigarsu wani mugun hannu da za a cutar musu da rayuwarsu.

Rahotanni na nuni da cewa, ɗaruruwan yara ‘yan aikatau ne a Nijeriya, suke fuskantar uƙuba kala kala a hannun iyayen gidan su, inda suke azabtar da su da bautar da rayuwar su, a kan ɗan abin da bai kai ya kawo ba. Wasu yaran ma ana sa su cikin rayuwar da ba ta dace ba, amma saboda ba a bari a na kai ƙara wajen ’yan sanda ko jami’an tsaro haka labarin ke shirirancewa babu matakin da ake ɗauka. Duk da dokar kare haƙƙoƙin yara da wasu jihohin Nijeriya suka sanya wa hannu, har yanzu hukunta irin waɗannan iyayen riƙo yana wahala.

A watannin baya mun ga yadda zaurukan sada zumunta suka cika da Allah wadai a kan wani mummunan al’amari da ya faru a Jihar Ondo, inda wata mata ta yanyanka hannun wani ƙaramin yaro da bai wuce shekaru goma ba, wanda ke masa aiki a gida, da reza, saboda yana zargin yaron da tsame masa naman miya. Alhalin daga baya an gano cewa, yana azabtar da yaron ne da yunwa, tana ba shi abinci sau ɗaya a yini, shi ya sa yaron ya ke lalubar duk abin da ya samu yana ci. Ban da wannan yankan reza ma da ake zargin an yi wa yaron, an kuma gano wasu tabon a jikinsa, saboda azabtarwar da ake yi masa.

Lallai ya kamata iyaye su gane haɗarin da suke jefa rayuwar ‘ya’yansu cikin wani mawuyacin hali, ta hanyar tura su aikatau wajen mutanen da ba su ma san su waɗanne iri ba ne. Yaya tarbiyyarsu ta ke, kuma yaya tausayi da kulawar su kan amanar da za su ba su. Mu sani fa yaran nan amana ce a wajen mu, kuma wajibi mu ne mu dage mu yi abin da ya dace. Kada mu riƙa kai su inda kima da mutuncin su za su tozarta.

Har wa yau, haƙƙin al’umma ne musamman maƙwafta su riƙa sa ido kan abubuwan da ke faruwa a kusa da su, kuma su tabbatar suna fallasa irin waɗannan abubuwan, domin akwai yanayin da idan abin ya bayyana, har su sai ta shafa, saboda kawar da kai da kuma shirun da suka yi. Lallai ne a nemi shawarwarin lauyoyi da ‘yan sanda wajen ganin ana bin kadin irin wannan ayyukan cin zarafi da mugunta da ake nuna wa yaran wasu.