
Daga BELLO A. BABAJI
Babban jami’i kan Nazarin Ayyukan sojoji a Hedikwatar Tsaron Nijeriya, Manjo-Janar Adekunle Ariyibi ya ce wasu ƙungiyoyin ƙasashen wajen suna ɗaukar nauyin Boko Haram da wasu ƙungiyoyin ta’addanci.
Babban sojan ya bayyana hakan ne a yayin hira da gidan talabijin na ‘channels’ a yau Litinin, inda ya ce a dalilin haka ne yaƙi da ayyukan ta’addancin ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP ya ƙi ƙarewa.
Ya ce, babu kokwanto akan haka ganin yadda a tsawon shekaru 15 ko sama da haka an gagara kawo ƙarshen ta’addancin mayaƙan ƙungiyoyin.
Ya ƙara da cewa, sanannen abu ne cewa ayyukan Boko Haram da ISWAP ya bunƙasa ne tun lokacin da suka fara alaƙanta kansu da ISIS wanda hakan yasa suke samun agaji daga mataki na ƙasa-da-ƙasa, lamarin da ya wa Nijeriya girma.
Manjo-Janar Aribiyi ya ce za a fahimci abinda ya ke faɗa duba da irin makaman da ƴan ta’addar suke amfani da su da ire-iren salonsu na kai farmaki.
A kwanan nan ne aka samu wani ɗan majalisa a Amurka mai suna Scott Perry, wanda ya ce Hukumar Amurka ta Tallafa wa Ci-gaba a matakin Ƙasa-da-ƙasa (USAID) tana ɗaukar nauyin ƙungiyoyin ta’addanci ciki har da Boko Haram.