A gaggauta hukunta waɗanda suka kashe Sheikh Aisami – JIBWIS

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ƙungiyar Jama’atul Izalatul Bid’ah wa Ikamatis Sunna a Nijeriya JIBWIS, ta yi kira ga mahukuntan ƙasar da su “gaggauta” yin hukunci ga wasu sojojin ƙasar biyu da ake zargi da kisan Sheikh Goni Gasua Aisami.

Rundunar ‘yan sandan jihar Yobe da ke Arewa maso gabashin Nijeriya, ta sanar da kama wasu sojoji biyu, waɗanda ake tuhuma da kashe Aisami a ranar Juma’ar da ta gabata.

Shugaban ƙungiyar ta ƙasa Sheikh Abdullahi Bala Lau ne ya yi kira ga mahukuntan kamar yadda wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar a shafinta na Facebook a ranar Litinin ta nuna.

Aisami na hanyarsa ta komawa garin Gashua daga Kano ne a lokacin da lamarin ya faru, inda wani soja ya nemi ya rage masa hanya, daga bisani kuma sojan ya bindige malamin har lahira ya kuma yi yunƙurin guduwa da motarsa.

“Shugaban JIBWIS Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta ɗaukar mataki akan wasu sojojin Nijeriya guda biyu da suka kashe caya daga cikin malaman ƙungiyar Sheikh Gwani Aisami da ke garin Gashua ta jihar Yobe.

“Muna yaba wa hukumar ‘yan sanda da suka ɗauki mataki nan take na cafke sojojin da aka samu a daji wajen gawar marigayin,” inji Sheikh Bala Lau.

Sheikh Bala Lau ya kuma ce babu shakka ƙungiyar ba za ta amince akan wannan “ta’addanci ba,” yana mai cewa “sun zura ido da kunnuwa domin sauraren yadda za ta kaya wajen aiwatar musu da hukunci cikin gaggawa.”

Kakakin rundunar ‘yan sanda a Yobe, Dungus Abdulkarim, wanda ya tabbatar da kama sojojin, ya kuma ce bayan kammala bincike zai yi ƙarin bayani kan wannan al’amari.

Jaridar Premium Times ta bayyana cewa Abdulkareem ya ce sojojin sun amsa laifin kashe shehin malamin.