A game da zaɓen Turkiyya

Daga ABDULAZIZ T. BAKO

A ranar Lahadin da ta gabata ne aka gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da ‘yan majalisu a ƙasar Turkiyya. Zaɓen ya jawo hankalin al’ummatai daban-daban a faɗin duniya.

A Najeriya, musamman a Arewa, al’ummar musulmi da dama suna kallon zaɓen a matsayin wani zaɓe da yake gudana tsakanin musulunci da kafirci. Sai dai shi wannan irin tunani na addinantar da wannan zaɓen bai yi la’akari da sarƙaƙiyar da ke tattare da shi wannan zaɓen ba da kuma ainahin tarihin ƙasar Turkiyya.

Wasu suna ganin cewa kamar taron dangi ƙasashen duniya suka yi wa shugaban ƙasar yanzu, Recep Tayyip Erdogan, don ganin sun kayar da shi. Amma babban abinda na fi so masu karatu su fahimta shi ne cewa l, mutanen ƙasar Turkiyya su suka fi kowa sanin abinda ya dace da su, halin da ƙasarsu take ciki, da shugaban ƙasar da ya kamata su zaɓa. Abin sha’awar kuma shi ne cewa, zaɓensu zaɓe ne mai inganci sosai. Wanda ya ci, shi za a bawa.

Tabbas Erdogan ya yi kokari sosai wurin dawo da ƙarfin addinin musulunci a Turkiyya, bayan ragargaza shi da Mustapha Kamal Ataturk ya yi na tsawon shekaru, wanda wannan illar da shi wannan talikin ya yi wa musulmai a lokacinsa ne ya sa addinin Musulunci yake da rauni a Turkey. Wani ƙiyasi ya nuna cewa, sama da kaso 95 cikin 100 na mutanen ƙasar Turkiyya suna ikirarin su Musulmi ne, amma ƙasa da kaso ishirin cikin 100 ne na mutanen ƙasar ke bin musulunci a aikace, kamar yin sallah da azumi da sauransu.

Za ka ga da dama mata suna iƙirarin su musulmai ne amma babu ruwansu da hijabi ko ɗan kwali. Ƙaramin siket ɗinsu suke sawa, su je duk inda suka ga dama. Sallah kuwa dama ba kowa ba ne yake tsayar da ita ba.

Kaɗan daga cikin irin ayyuka na kassara addinin musulunci da Ataturk ya yi sun haɗa da haramtawa mutane kiran sallah da yin karatun sallah da larabci, komai sai dai a yi shi da yaren Turkiyya. Ya ɗabbaƙa ɗabi’ar rashin saka hijabi ta hanyar uzzurawa mata masu saka hijabi a hukumance. Ya rufe masallatai da makarantun addini. Ta kai ta kawo cewa a lokacin a boye ake koya wa mutane karatun Alƙur’ani domin idan aka gano mutum yana koyar da Ƙur’ani, to ya bani.

Har bayan mutuwar Ataturk wannan tsari nasa ya ci gaba da wanzuwa a Turkey, duk da an samu mutane masu bin tafarkin Ataturk irin su Adnan Menderes da suka dawo da gina masallatai da kuma kiran sallah da larabci a shekarun 1950 zuwa 1960. Amma musulunci bai fara samun ƙarfafa a Turkiyya, ba har sai wurin shekarun 1980s da aka fara samun manyan ‘yan siyasa masu bin tafarki irin wanda Erdogan yake a kai suna iya fitowa su nuna muhimmancin musulunci a rayuwar Turkawa da kuma kokarin dawo da Turkiyya kan turbar addinin musulunci, wanda da kaɗan-da-kaɗan suka samu ƙarfi har suka karvi mulkin ƙasar.

A halin yanzu wanda suke takara da Erdogan, wato Kemal Kilicdaroglu, mabiyin ra’ayin Ataturk ne na ga ni kashe ni. Shi ya sa a yayin da shi Erdogan ya rufe yaƙin neman zavensa a masallacin da Hagia Sophia, shi Kemal Kilicdaroglu a wurin ziyarar kabarin Ataturk ya rufe yaƙin neman zaɓensa.

Wannan shi ya sa musulmai da dama suke fatan Erdogan ya ci gaba da mulkar ƙasar saboda kada shi wannan mutumi ya karɓi ƙasar ya dawo da musulunci baya. A gefe guda shi kuma Erdogan, ya fuskanci matsalolin rugurgujewar tattalin arzikin Turkey a ƙarƙashin mulkinsa, wanda hakan ne ya sa wasu suke zargin cewa amfani yake da musulunci wurin rufe tabargazar da gwamnatinsa ake zarginta da yi.

Ko ma dai menene, Allah ya yi wa ‘yan ƙasar Turkiyya zaɓin shugaba nagari. Ameen.

Abdulaziz T. Bako (MBBS, MPH, PhD), ɗan Nijeriya ne mazaunin ƙasar waje. Mai sharhi ne a kan lamurran yau da kullum.