A karo na biyu cikin 2025, rumbun lantarki na ƙasa ya lalace

Daga BELLO A. BABAJI

A ranar Juma’a ne ƴan Nijeriya suka sake samun kansu a yanayi na duhu sakamakon tsaiko da rumbun wutar lantarki na ƙasa ya samu a wani wuri karo cikin 2025.

Manyan kamfanonin raba lantarki na Ikeja da Eko sun tabbatar da aukuwar lamarin, wanda ya faru da misalin ƙarfe 4 na yamma.

A sanarwar da Kamfanin raba Wutar lantarki na Ikeja ya yi ta shafin X, ya shaida wa kwastomominsa cewa, sun samu tsaiko ne tun daga ƙarfe 2 na rana, amma jami’ansu da haɗin-gwiwar masu-ruwa-da-tsaki na aikin gyarawa.

Haka ma na Eko, wanda ya ce sun samu ƙarancin wuta daga Kamfanin Wutar lantarki na Ƙasa (TCN), inda ya ce suna bin matakan da suka dace wajen shawo kan matsalolin da suka haifar da tsaiko.

Lamarin ya auku ne a yayin da al’umma ke jimamin ƙarin farashin lantarki da aka yi da ƙoƙarin raba wadataccen wuta ga dukkanin sassan Nijeriya da ma’aikatar lantarki ke yi.