Daga BELLO A. BABAJI
Pep Guardiola ya sha kaye har sau huɗu a jere a tarihin kasancewar sa koci bayan da ƙungiyar Brighton da doke Manchester City da ci 2 da 1 a ranar Asabar.
Ɗan wasan gaba na Manchester City, Erling Haaaland shi ya fara zura ƙwallo a ragar Brighton inda daga baya Jao Pedro ya farke.
Ƙasa da mintina 15 kan a tashi ne ɗan wasan Brighton, Matt O’Riley ya zura ƙwallo ta biyu a ɓangaren da Guardiolan ke jagoranta.
Guardiola dai ya jagoranci ƙungiyoyin Barcelona da Bayern Munich a baya inda wannan shi ne karo na farko da ya sha kaye sau huɗu a jere.
Haka kuma, wannan shi ne karo na farko da irin hakan ke faruwa da Manchester City tun a shekarar 2006 a lokacin koci Stuart Pearce.
Sauran ƙungiyoyin da suka casa ƙungiyar sun haɗa da; Tottenham Hotspur a wasan kofin ƙalubale, Bournemouth a wasan Firimiya (wanda shi ne kayenta na farko a gasar tun Disambar 2023), sai kuma Sporting Lisbon da ta lallasa ta da ci 4 da 1 a gasar zakarun Nahiyar Turai a tsakiyar mako.
Ana ganin hakan na faruwa da ƙungiyar ne sakamakon raunuka da ƴan wasanta da dama suka samu waɗanda suka haɗa da; Kevin De Bruyne, Nethan Ake da Manuel Akanji.
Sauran sune Rodri, wanda shi ne ya lashe kyautar Ballon d’OR ta bana, Ruben Dias, John Stones, Jeremy Doku da kuma Jack Grealish.