A karon farko an naɗa mace Alƙalin-alƙalai a tarihin Kano

Daga BASHIR ISAH

A ranar Alhamis da ta gabata Majalisar Dokokin Jihar Kano ta tabbatar da naɗin Dije Aboki a matsayin Alƙalin-Alƙalan Jihar Kano.

Wannan naɗi ya zama al’amari na tarihi a jihar, kasancewar Dije ce mace ta farko da za ta riƙe wannan matsayi a jihar ta Kano.

Naɗin nata ya biyo bayan wasiƙar da Gwamna Abba Yusuf ya aike wa majalisar jihar wadda aka gabatar da ita a zauren majalisar a ranar Alhamis.

Shugaban Majalisar, Ismail Falgore, shi ne ya karanto wasiƙar yayin zaman majalisar a ranar Alhamis da ta gabata.

Da fari, an naɗa Dije Muƙaddashin Alƙalin-alƙalan jihar ƙarƙashin tsohuwar gwamnatin Abdullahi Ganduje.

Majalisar ta yaba da naɗin Dije tare da kira a gare ta da ta zage dantse wajen yi wa fannin shari’ar jihar aiki tuƙuru.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *