A karon farko Jihar Kogi ta samu kasonta a matsayin jihar da ke da arzikin man fetur a Arewacin Nijeriya

Shugaba Buhari da Gwamna Bello

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

A karon farko Jihar Kogi ta fara samun kasonta a matsayin jiha mai arzikin man fetur a Arewacin Nijeriya.

Jaridar yanar gizo ta Intelregion, ta rawaito Gwamna Yahaya Bello yana bayanin cewa gwamnatin jiharsa ta karɓi kaso daga cikin kashi 13 da ake ware wa jihohi masu mai.

Yahaya Bello ya yi wannan bayani ne a wajen taron Majalisar Zartarwa na jiha wanda aka saba yi duk mako a gidan gwamnati na Lugard House.

Gwamna Bello ya ce gwamnatinsa ta yi abubuwan a-zo-a-gani, inda ya ce samun arzikin mai zai taimaka wajen cigaba da kawowa mutanensa cigaba.

A cikin jawabin nasa da jaridar ta haƙaito, gwamnan ya nuna farin ciki da wannan nasara da jihar ta samu. A cewar Bello, gwamnatinsa ta samu lambar yabo da kyauttuka iri-iri saboda yadda suke tafiyar da mulki ƙeƙe-da-ƙeƙe kuma cikin gaskiya da amana.

“Mun sha wahala wajen kafa tarihin nan. Ba don gudunmuwar mutanenmu da suka tsaya mana ba, da ba za mu iya kai wa ga nasarar nan ba. Muna miƙa godiyarmu ga Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari da jagorancin da ya yi, da kuma RMAFC da ta sa wannan ya tabbata.”

Gwamnan ya yi alƙawarin amfani da dukiyar da aka samu wajen gina makarantu, asibitoci, da tituna, sannan a tallafa wa marasa ƙarfi tare da inganta tsaro.

Kwamishinan yaɗa labarai na Jihar Kogi, Kingsley Fanwo ya ce kuɗin sun fara zuwa ne a lokacin da gwamna yake yin ayyukan da za a tuna da shi nan gaba.

Hukumar RMAFC mai kasafin dukiyar ƙasa da albashi ta sa Kogi a matsayin jihar da take da arzikin mai, don haka za ta riƙa amfana da kashi 13 cikin ɗari duk wata.

Dama can an yi alƙawari jihar za ta fara karɓar kasonta a wannan kuɗi idan rijiyar man Ibaji ta fara aiki, kuma yana kawo wa asusun tarayya kuɗin shiga.