A na ci gaba da ɗaukar shirin ‘Zo Mu Zauna’ Zango na uku

DAGA MUKHTAR YAKUBU

A yanzu haka dai an ci gaba da ɗaukar shirin fim ɗin ‘Zo Mu Zauna’ mai dogon zango wanda a ke shaska shi a tashar Rarara da ke Kan YouTube wanda fitaccen marubucin labarai, kuma Furodusa Naziru Alkanawy yake ɗaukar nauyin shirya shi.

Ko da yake tun bayan kammala zango na biyu mutane da suke bibiyar shafin na YouTube na Rariya domin kallon fim ɗin suke ta tambaya a rashin ganin fim ɗin, wanda hakan ya sa a ke tambayar ko dai fim ɗin an jingine shi ya tafi hutun dole?

A yanzu dai an ci gaba da ɗaukar shirin zango na uku wanda nan gaba kaɗan bayan kammala aikin za a ci gaba da haska shi domin jama’a su ci gaba da kallon shirin.

Naziru Alkanawy shi ne mai shirya fim ɗin wanda a cikin tattaunawar da muka yi da shi a dandamalin ɗaukar fim ɗin ya shaida mana cewar,

“To Alhamdulillahi, a yanzu aikin yana tafiya bisa tsari duk da dai ka san a yanzu gari na Damuna sai ka tsara abin da za ka yi sai yanayin ruwa ya sa a samu matsala.

“Kuma idan muka kwatanta da aikinmu na baya za mu ga an samu ci gaba sosai, kuma nasarar da muka samu a baya, daga masu kallo wanda ya kai ci gaban da ba mu zata ba ita ce ta ba mu qarfin gwiwar ci gaba da aikin a yanzu.

“Kuma an ɗauki lokaci mai tsawo a na yin shirye shirye, wannan ya sa aka daɗe ba a gani ba, amma dai mun yi hakan ne domin mu samar da aikin da zai gamsar da mutane. Kuma muna sa ran in Allah Ya yarda zuwa wata na gaba mu fara saka shi don jama’a su gani.

“Burinmu dai shi ne, shawara da mutane suka ba mu da gyara bayan sun kalli zango na ɗaya da na biyu su gamsu cewa mun karɓa.

Don haka muna godiya ga masu biyiyarmu da haɗin kan da suke ba mu, wanda hakan ne ya sa muka ci gaba da shirya fim ɗin.”

Shi ma fitaccen jarumi, kuma Darakta, Ishaq Sidi Ishaq, wanda ɗaya ne daga cikin jaruman shirin ya bayyana cewa, “Shi wannan fim ɗin na ‘Zo Mu Zauna’, ya nuna an samun ci gaban zamani a masana’antar finafinai ta Kannywood, domin idan ka auna yadda harkar ta ke a baya a na yin ta ne a bisa matakin koyo.

“Amma a yanzu an samu ci gaban zamani da kuma kayan aiki masu inganci. Kuma kamar yadda kake gani, ni Ina matsayin jarumi ne a wannan fim ɗin, don haka Ina kallon kaina a matsayin jarumi kamar yadda aka nemeni na zo na yi aikin, kuma yadda na ga a na ɗaukar fim ɗin ya yi mini daidai a matsayina na jarumi, kuma duk abubuwan da ya kamata a yi a wajen shirya fim Ina ganin a na ƙoƙarin kwatantawa.

“Ina ganin haka ya samu ne saboda ɗaukakar shirin ‘Zo Mu Zauna’ ya samu a wajen masu kallon sa a YouTube. Don haka duk lokacin da ka ga fim ya samu karɓuwa, to akwai abubuwa da aka kamanta na gaskiya. Ina ganin waɗannan su ne dalilan da suka sa a ke ganin ci gaba a finafinanmu na wannan lokacin.”

Shi ma jarumin fim ɗin Ɗanlladi, wato Bilal Mustapha ya bayyana mana cewar a matsayin sa na jarumi fim ɗin ‘Zo Mu Zauna’ shi ne ya zamo silar ɗaukakar sa a duniya. Domin kafin a saka shi a cikin sa, sai dai ya fito sin ɗaya, sin biyu. Amma sai ga shi ya fito a matsayin jarumi wanda ya samu ɗaukaka a duniya, saboda haka ya na jin daɗin rol ɗin da yake takawa.

Ita ma jarumar fim ɗin, Saratu Muhammad, wadda ta fito a matsayin Hajiya Baraka. Ta bayyana cewar abin da ya fi burge ta a fim ɗin shi ne, yadda take taka rol ɗin babbar mace wadda har ta aurar da ‘ya, kuma ga shi a matsayin ta budurwa da ko auren fari ba ta yi ba, don haka matsayin ya ɗaga mata darajar a wajen mutune a duk in da ta je.

A yanzu dai za a iya cewa, fim ɗin ‘Zo Mu Zauna’ ya shiga jerin finafinan da masu kallo suke bibiyar sa a shafukan YouTube a cikin finafinan da a ke yi a masana’antar Kannywood.