Ba ni da jam’iyya a yanzu, amma ina goyon bayan wasu ‘yan takara – Dogara

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara ya ce shi ba ya cikin jam’iyyar siyasa a yanzu amma yana goyon bayan ’yan takara a faɗin jam’iyya ne kawai don neman muƙamai a zaɓen 2023 mai zuwa.

Dogara, wanda ke wakiltar mazaɓar Dass/Tafawa Balewa/Bogoro a zauren majalisar tarayya, ya yi magana a shirin siyasa na gidan talabijin na Channels a ranar Laraba wanda News Point Nigeria ke sa ido.

Ya kuma ce kasancewar yana goyon bayan ’yan takara na jam’iyyu daban-daban na kujeru daban-daban ba ya nufin cewa shi mutum ne mai “mara son kwanciyar hankali” kamar yadda masu zaginsa suka ce.

Dogara ya kasance sanannen jigo a Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) kafin zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa na jam’iyya mai mulki.

Tsohon kakakin ya kasance ɗaya daga cikin waɗanda suka yi kakkausar suka ga tikitin takarar Musulmi da Musulmi na jam’iyyar, inda daga baya ya fito fili ya nuna goyon bayansa ga ɗan takarar Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar a kan Bola Tinubu na APC.

Sai dai Dogara ya nuna adawa da sake zaɓen Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed na jam’iyyar PDP tare da bayyana goyon bayansa ga ɗan takarar gwamna na Jam’iyyar APC a zaɓen da za a yi a Bauchi a ranar 18 ga watan Maris, Air Marshal Sadique Abubakar, wanda shi ne tsohon babban hafsan sojin sama na Nijeriya.

Da aka tambaye shi ranar Laraba ko shi ɗan PDP ne ko kuma ɗan APC, Dogara ya ce shi ba shi da jam’iyya.

Ya ce, “Ina goyon bayan ’yan takara; Ba wata jam’iyya da nake yi a yanzu, Ina goyon bayan ’yan takara ne.

“Kowa ya san cewa na goyi bayan Atiku Abubakar ne a matsayin shugaban ƙasa saboda wasu dalilai da na shaida wa duniya baki ɗaya, amma a Jihar Bauchi, kafin a kammala zaven fidda gwani na goyi bayan mai son tsayawa takara, Air Marshal Sadique Abubakar, wanda shi ne ɗan takarar gwamna a Jam’iyyar APC a halin yanzu, kuma Ina da ‘yan takarara na majalisar wakilai da na majalisar jiha a mazaɓata.

“Ina da ‘yan takarar Sanata da na wakilai da na taimaka musu wajen yi musu uwa da makarviya a waɗannan muƙaman, kuma ba zan iya yin watsi da su ba don wani abu na siyasa.”