A Nijeriya ne kawai miji zai bushi iska ya kori matarsa daga gida gwamnati ta ƙyale shi – Uwani Kazaure

Laulayin ciki ne babban ƙalubalena a wurin aiki”

Daga UMAR AƘILU MAJERI

Hajiya Uwani tsohuwar malamar makaranta ce kuma masaniya akan yaren Turanci da Hausa. Ta kasance ɗaya daga cikin Mata ‘yan gwagwarmayar nema wa Mata da ƙananan Yara ‘yanci a Jihar Jigawa. 
Yanzu haka Hajiya Uwani ta fara tunanin kafa wata gidauniya mai zaman kanta saboda ta riƙa taimaka wa yara matan da aka ci zarafinsu, don ganin ta kare masu mutuncinsu kamar yadda sauran al’umma suke da. Wakilinmu na Jihar Jigawa, Umar Aƙilu Majeri ya samu nasarar zantawa da ita a gidanta da ke Dutse. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

MANHAJA: Mu fara da tarihin rayuwarki a taƙaice.
UWANI AHMED: Sunana Hajiya Uwani Ahmed Kazaure. An haifeni a garin Kazaure a shekarar 1976. Nayi karatun ‘primary’ a Kazaure, a kudu primary, a 1986. Da na gama, naje makarantar Mata ta Kazaure 1986. Daga nan na wuce makarantar Mata ta Garki 1990, a nan na kammala, a shekara ta 1992. An yi min aure a 1995. Daga nan na fara karatu a legal ta Ringim. Ban gama ba na bari. A shekara ta 1997 na kama aikin koyarwa a sabon gari  primary dake Ringim. Daga baya na sake komawa legal na karanci yaren Turanci da Hausa wato ‘language’ a 1999 zuwa 2002, nayi diploma ne ta wannan ɓangaren. Daga nan ne na kama aikin koyarwa a sakandiren ‘Yanmata ta Kazaure a matsayin malama.

Daga nan na koma karatu a Jami’ar Bayaro dake Kano. Na karanta ‘Hausa special’ na gama a 2008. Daga nan aka kaini ‘Unity school’ ta Gwaram, daga baya aka dawo dani makarantar Mata ta Ɓaure da ke nan Dutse, a matsayin malama, na kuma zauna a makarantar jeka-ka-dawo dake Galamawa a nan Dutse. Saboda ina fama da matsalolin ciki idan ina ɗauke da juna biyu shi ne nake samun matsala a wajan aikina, sadoda innaje asibiti likita yana bani hutu na kwanaki a gida, hakan yasa na riqa samun matsala a wajan aikina, saboda haka ne na ajiye aikin gwamnati domin na ba wa ‘ya’yana kulawar da ya kamata. Don haka na koma yin aiki da ƙungiyoyi wato NGOs.

Bayan na bar aiki da gwamnati, na koma yin aiki da PRRNNMCH. Abin mamaki albashin na su ma yafi na lokacin da na ke aikin da gwamnati. Saboda albashinsu dubu sittin ne a gwamnati, amma nan da na dawo albashinsu ya haura 200,000 a wata. A taƙaice dai har yanzu da muke fitar nan ina yin aiki da NGOs. Inda nayi aiki da NGOs da dama, kamar M4D wanda nayi aiki da su daga shekara ta 2014 zuwa 2015. Daga nan na koma MNCH2. Da na barsu shine na koma aiki da ‘Lafiya projects’. Duk da haka har yau ina aiki da ‘Vildec’, saboda su ne suke yin aiki don kare mutuncin yara mata da yaƙi da cin zarafinsu.

Waɗanne irin ƙalubale ki ka fuskanta a lokacin da ki ke aikin gwamnati?
Na samu ƙalubale masu yawa a wajan aikina, saboda na kasance mace mai larura a lokacin renon ciki, sau da yawa innaje asibiti likita ya kan ban hutun sati biyu wani lokacin hutun wata uku, hakan yasa shugaban makarantar da nake koyarwa a ƙarƙashinsa ya riƙa yin ƙorafi kaina, bana son zuwa aiki, a cewar sa. Sakamakon haka akayi ta kai ƙorafi kaina ma’aikatar ilimi, kan cewa ba na son zuwa aiki.

Irin nawa laulayin idan nayi doguwar tafiya sai in fara zubar jini. Wannan ne dalilin da yasa likita ke sani zaman hutu. Amma saboda shi wannan malamin bai san halin da nake ciki ba, gani yake yi kamar ina haɗa baki ne da likitocin suke rubuta min hutun. Don haka ganin koke-koken yayi yawa ne yasa na ajiye aikin koyarwa na kama aiki da ƙungiyoyin da ba na gwamnati ba. Kuma hakan sai yafi min alkhairi, domin ina da lokaci.

Mene ne burinki a rayuwa?
Babban burina bai wuce na kafa wata gidauniya da zan riƙa taimakawa Mata da yara ƙanana musamman yara mata da aka ci zarafin su. Sannan ita wannan gidauniyar in sa mata sunan mahaifina.

Kamar ƙasashe nawa ki ka je?
Eh to, na je Saudiyya har sau huɗu. Naje Nijar, Kamaru, Sudan, Chadi kuma naje Maleshiya.

Daga cikinsu wace tafi burge ki?
Ƙasar Maleshiya ce tafi burgeki, saboda suna da dokoki. Ƙasarsu ba a yin zaman banza. Ba tuƙin ganganci. Kuma ko wacce unguwa akwai tashar mota, motar wata unguwa bata lodi a tashar wata unguwa. Gaskiya yanayin tsarin su, da bin dokokin gwamnati yafi komai burgeni.

Makarantun su da asibitocin su gwanin sha’awa. Misali idan kaje asibiti likita yace ka dawo gobe, idan bai ganka ba, zai kiraka yaji ko lafiya. Kuma da bai same ka ba, zai yi tataki har gidanka don samun tabbacin lafiyar ka. Makarantunsu komai cikin tsari, komai a wadace, ba a sace kayan karatu, saɓanin makarantunmu da wasu malaman marasa kishi kan sace kayan gwamnati suna sayarwa.
Maleshiya ƙasa ce da suke bin doka. Dole ne duk matsayinka kabi doka, baka isa ka karya doka ba. Saɓanin Nijeriya ƙiri-ƙiri saboda gadara kaga mutun yayi aron hannu a tuƙi, ko kaga mutun ya zauna a gefen titi, ya juyawa titi baya duk wannan rashin bin doka ne da ba zaka taɓa ganin haka ba a can. Gaskiya tsarinsu yana burgeni.

An ce suna yin miya da ƙaguwa da kwaɗi kasancewar wasu daga cikin mazauna ƙasar ‘yan Chana ne, kuma al’adarsu iri ɗaya ce. Shin ko kin samu kanki a ɗanɗana irin waɗannan kayan daɗin?
(Dariya) Ai ba kowa ne ya ke cin kwaɗi ba, kuma ni wajan da na zauna da mijina wani gida ne da muke tare da mutanen chana da Indiya. Amma mafi yawansu Musulmai ne. kuma muna yin mu’amala da juna, amma magana ta gaskiya ba komai ne muke ci ba.

Yaya al’adarsu ta ke a can?
A can dai mace batayin goyo irin tamu al’ada. Domin na taɓa goyon yarona zanje kanti, ina tafiya sai naga mutane suna ta bina, kan kace kwabo jama’a sun cika titi ana ta ɗaukar hotona. Da na shiga kantin da zanyi siyaya, nake tambayar mai kantin, ko me yasa ake ta bina? sai tace, “ai saboda wannan goyan ne, domin kinzo da sabon abu damu bamayi, kuma in ki ka fita haka zasu biki har gida.” Shine da zan fita sai na sauke yarona a ƙasa na ja hannunsa har muka koma gida. Kamar yadda suke yi a can. Ƙasar Maleshiya ƙasa ce mai tarin al’adu, don sun haɗa mazauna da yawa, amma hakan ba yana nufin don ka je ba sai ka yi duk abin da ake yi ko ake ci ba.

To mu yi maganar irin abincin da ki ka fara ci a can.
Gaskiya ba komai nake ci ba, da ya ke mun je da kayan abincinmu na nan gida, amma duk da haka muna amfani da wasu kayan abincinsu kamar biredi, shayi, kwai, dankali da sauransu.

Ya suke yin aure a can?
Su fa aure baya mutuwa a can sai da dalili. Sau da yawa ma sai dai kotu ta raba auren, ba kamar namu ba, mutum idan ya shaqi iskar duniya ya kori matarsa tare da ‘ya’yansa, ya auri wata, kuma ba abin da za a yi. A can gwamnati ce zata koreshi daga gidan, ta baki, wannan dokar haka take a Chadi da Sudan.

Wani abin birgewa wurin waɗannan bayin Allan shine, suna bada damar ka bambance matar aure da budurwa ko bazawara, ta yadda ba za a samu irin kutse na mazan zamani ba. Wannan ne zai sa kasan matar da za ka iya taro don nemanta. Ta ya ake ganewa. Matar aure bata fita da dare, zasu barwa marar aure wannan lokacin. Su kuma zawarawa da ‘yammata basa sanya lifaya, ko suyi lulluvi. basa sanya zobe. Ta haka ne ake bambance matar aure da marar aure, domin nima kafin na dawo sai da adon lifaya ya fara shiga jikina, ya fara zama min jiki.

Da ya ke kin ce kin tava zama a Chadi, ya suke gudanar da bikin aure?
Su a Chadi miji ne ya ke yin komai, domin hatta turaren amarya miji ne ya ke saya. Haka abinci da za a yi ranar bikinsa a gidan Amarya da gidansu shine zai saya, iyayan amarya basa yin komai, saɓanin tamu al’adar, idan za kayi auren ‘yarka sai kayi kamar zaka ce wayyo Allah saboda abinda muka ɗora wa kanmu na al’ada.

Wane abinci ne ki ka fi so?
Na fi son danbun kuskus, sai tuwo miyar kuka ko shinkafa da miya.

A ɓangaren kwalliya wacce shiga ce ki ka fi son yi?
Ni ba ni da wata kwalliya da tafi adon atamfa. Ban damu da wata kwalliya irinta zamani ba, domin kwalliya yanzu sai dai na yi wa kaina.

Batun iyali fa?
Ina da yara biyar; mata uku, maza biyu. Dukkansu suna karatu; wasu suna jami’a, wasu a sakandire, ɗaya yana firamare.

Hajiya, mun gode sosai.
Ni ma na gode matuƙa.