Asslama alaikum. Barka da Juma’a, ’yan uwa musulmi.
A farko dai, daga cikin alamomin da ake iya kula a gane mutum na dauke da wannan damuwa, ko kuma a ce hankalin sa ya fara tavuwa, a cewar wani ƙwararren likitan ƙwaƙwalwa, Dr Maigari Yusuf Taru, idan aka ga halayyar mutum na canja wa daga wani yanayi da aka saba da shi zuwa wasu halaye da ba san shi da su ba, kamar idan an ga mutum mai tsafta ya fara zama ƙazami, ko mutum mai shiru-shiru, a ga ya koma magana barkatai, ko idan yana da son shiga jama’a sai a ga lokaci guda ya koma keve kansa yana gudun jama’a. Ko kuma a ji mutum na yawan zargin wasu na shirya masa mugunta ko neman ganin bayansa.
Shugaban ƙungiyar ƙwararrun masana ilimin ɗabi’ar ƙwaƙwalwar ɗan Adam ta Nijeriya Farfesa Taiwo Obindo ya bayyana damuwa kan yadda ake samun yawaitar masu fama da lalurar ƙwaƙwalwa a Nijeriya, inda ya bayyana cewa kawo yanzu akwai ‘yan Nijeriya kimanin Miliyan 60 da ke fama da wannan matsala, kuma yawan cin su suna rayuwa ne cikin jama’a, wanda aka danganta da halin taɓarɓarewar tattalin arziki da ƙuncin rayuwa da ake fuskanta.
Masana harkar lafiya na ganin matsaloli na rayuwa, shaye-shayen magunguna barkatai, ƙwayoyin halitta na gado da shan sinadarai masu ƙarfi ko karayar zuciya, a dalilin ɓacin rai na daga cikin dalilan da suke kawo tavuwar ƙwaƙwalwa. Kuma a cewar ƙwararru ana iya samun lalurar ƙwaƙwalwa tun daga ciki kafin a haifi mutum, sakamakon wasu dalilai na ganganci ko kuskure ko wasu magunguna da mai ciki ta ke sha wanda zai iya rikita ƙwaƙwalwar jaririn da ke cikinta.
Mutane na iya kamuwa da lalurar ƙwaƙwalwa saboda shekaru ko yawan mu’amala da zaurukan sada zumunta yana iya shafar tunanin mutum da yanayin rayuwarsa, saboda yana ganin wasu ba sa ƙaunarsa ko ba a nuna masa ƙauna, ba a yi masa sharhi ko tsokaci a abubuwan da ya ke ɗorawa a giza gizan sadarwa da ya ke amfani da su. Bincike ya nuna cewa, yawan mu’amala da shafukan sadarwa yana haifar da matsalolin damuwa, fargaba, tsoro, da karayar zuciya, a sakamakon yadda mutum ke ganin yadda shafinsa na sadarwa ke jan hankalin jama’a ko akasin haka.
Har wa yau kuma yadda wasu ke nuna irin jin daɗin da suke yi da matsayin su a idon duniya, yana sa wasu su ji ƙasƙanci a ransu, har abin ya fara sa suna jin haushin kansu ko kunyar bayyana kansu, don kada a yi musu tunanin kimar su ba ta kai ba.
Yawan shaye-shaye a tsakanin matasa maza da mata misalin Shisha da ake ganin ba komai ba ce, bincike ya gano tana ɗauke da sinadaren da ke tava lafiyar ƙwaƙwalwa, tana kuma zama ƙalubale ga cigaban rayuwar matasa da makomarsu, a matsayin su na manyan gobe.
Wani tsohon shugaban ƙungiyar likitoci ta Nijeriya ya taɓa bayyana buƙatar Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa ta INEC ta sa a riƙa yi wa ‘yan siyasa masu fitowa takarar muqamai daban-daban gwajin lafiyar ƙwaƙwalwa, saboda tabbatar da ingancin lafiyarsu lura da irin yadda wasu ‘yan siyasa ke wawurar dukiyar ƙasa da almubazzaranci, wanda ya sava da aiki da hankali.
An yi kira ga hukumomin da abin ya shafa su riƙa ba da muhimmanci ga al’amarin kula da lafiyar ƙwaƙwalwa, samar da tallafin magunguna da inshorar lafiya, buɗe rassan kula da masu fama da lalurar ƙwaƙwalwa a ƙananan asibitoci na ƙauyuka da karkara, domin ƙara kusanto da harkar kula da lafiyar ƙwaƙwalwa ga jama’ar da ke ƙauyuka da karkara.
Sannan ana buƙatar iyaye da ‘yan uwa su riƙa gaggawar ɗaukar matakin neman magani da shawarwarin likita yayin da suka lura da canji a rayuwar wani makusancin su tun kafin abin ya fita daga matakin da za a iya gyarawa ko dawo da shi daidai.
A guji nuna ƙyama ko tsangwama ga waɗanda ke cikin wannan hali, a nuna musu ƙauna da kulawa, don haka ne zai sa musu natsuwa da yarda a zukatan su, har su amince su iya ba da haɗin kai a samar musu da magani da kulawar da ta kamata.
Wasiƙs daga MUHAMMAD AWWAL (Ya Muha), +2348062327373.