A saka hankali yayin zaɓin aure

Assalam alaikum. Da fatan kowa ya yi sallah lafiya? Allah ya albarkaci jaridar Blueprint.

A yau zan yi wasiƙa ne a kan zaɓin ma’aurata, domin shi ne babban abin da ke ci wa kowa tuwo a ƙwarya a halin yanzu. Wanda kuma hakan ke jawo yawan mace-macen aure, domin ana auren ne kawai barkatai ba tare da sanin wa ya kamata a aura ba.

Babban hadafin da ya ke sanya mu zaɓar wanda zamu rayuwa da shi ko wacce zamu rayu da ita a matsayin rayuwar aure shi ne samun nutsuwar rayuwa, shi kuwa samun nutsuwar ruhi da abokiyar zama ba ya yiwuwa sai ta hanyar auratayya, domin idan zaman rayuwar tare ya kasance ta hanyar fasiƙanci ne ba za a samu wannan nutsuwar ba har abada kamar yadda hakan ya tabbata a ilimance. Saboda haka duk wanda zai yi aure ya tuna ko ta tuna cewa za ta yi aure ne da wanda zasu zauna domin gina rayuwa marar iyaka da gina gida salihi. Amma tambaya a nan ita ce; Wane mutum ne zamu zaɓa domin wannan rayuwa da kuma samun nutsuwa, soyayya, tausasawa, da tausaya wa juna?

Lokacin da aka tashi neman abokin zaman tare yaya ya kamata a zaɓi juna? Mene ne ma’auni wajen zaɓar wanda za a aura? Da wace fuska zamu fito wa wanda zamu zaɓa? Shin yana daga cikin sharaɗi sai mai kuɗi, shaidar digiri, gwarzo, ko mai muƙami, ko kuwa? Kowane mutum yana da natsa sharuɗa da dokokin ko siffofin wanda ya ke so. Sai dai addini yana ƙarfafa kamalar mutum ta kasance ita ce hadafin zaɓarsa, wannan kamalar kuwa yawancin ruwayoyi suna nuni da cewa kamala ce ta kyawawan halaye da tarbiuyar addini a matsayin abin dubawa na farko, sannan kuma sai sauran siffofi kamar na iya ɗaukar nauyin wacce zai aura su biyo baya.

Idan muka bi hanyoyin da ake fuskantar abokin zaman tare da shi yayin zaɓarsa zamu ga wasu suna shigowa ta hanyar karairayi, sai su riƙa zuwa da fuskokin da ba haka suke ba, yaudara a nan ita ce ta yi fice. Yayin zavar abokin rayuwar aure kada a yaudari juna kamar yadda samari suke yi, sai ya ari agogo, da takalmi, da mota, da ƙaryar aiki, da karatau a jami’a, da tafiye-tafiye, wannan bai halatta ba, domin kamar yadda aka hana mace canja kama da zata sanya ta yaudari masoyi haka ma namiji bai halatta ba ya yaudare ta, haramcin yaudara ya shafi duk vangare biyun.

Zavar abokin zama ba kamar zaɓar riga ko mota ba ne da za ta tsufa a yar, a sake wata, abin ba haka ba ne, don haka iyaye su san wa ya ke zuwa wajen ’yarsu? Kuma wa za ta aura? Matuƙar mumini ne to su ba shi, sannan kada su dage a kan wanda ba ta so, ko sai mai kuɗi ko mai matsayi. Zaɓar abokin zaman aure yana da muhimmanci matuƙa, kuma idan ba a yi dace ba to rayuawr aure takan kasance da cutuwa ta zama tamkar kurkuku. Idan abokin zaman aure ba shi da siffofi na kamala yakan sanya gida ya zama azaba maimakon rahama da tausasawa.

Idan mace ba ta dace da miji ba to ta shiga uku, wahalar rayuwa da za ta faɗa ciki tana munana, sai ta sussuke ta koma tamkar ƙashin da aka tsotse. Haka nan ma namijin da bai dace da mace ba ya gama rukurkushewa, baqin ciki zai kasance tare da shi har sai ya tsufar da shi. Muhimmancin wannan lamarin ne ya sanya muka ga mai daraja da ɗaukakar Annabin Rahama yana addu’a yana cewa, “Ya Allah! Ina neman tsarinka daga matar da za ta sa ni yin furfura tun kafin lokacin tsufana”.

Zaɓar Mace;

Aure ba alaƙa ba ce mai rauni ko abota ta wani ɗan lokaci kamar yadda ya ke a al’adun wasu yankuna na yammacin duniya, kuma ba kamar alaaa ba ce takanin mutum da rigarsa, gidansa, ko abin hawansa. Shi alaƙa ce mai dawwama a wannan duniyar don taimaka wa juna a rayuwa da addini, wannan kuwa shi ne asasin gina iyali da al’umma za ta tsattsafo ta cikinsa. Don haka ne ruwayoyi masu yawa suka zo domin su gaya wa namiji siffofin macen da ya kamata ya rayu da ita.

Wani mutum ya zo wurin Imam Ja’afar Assadik(AS) yana gaya masa cewa, “Matata ta mutu, ta kasance mai dacewa da ni, kuma yanzu ina da niyyar yin wani auren. Sai ya ce da ni; Duba inda za ka sanya kanka, wacce za ka yi tarayya da ita a dukiyarka, ka nuna mata addininka da sirrinka, idan kuwa zaka yi hakan, to ka riƙi budurwar da ta ke dangantuwa zuwa ga alheri da kyawawan halaye. Ka sani cewa mata suna da halaye daban-daban, akwai wacce ta ke ganima ce, akwai wacce ta ke kamar jinjirin wata yayin da ya ɓullo ga mai shi, akwai wacce ta ke duhu ce. Wanda ya dace da ta gari to ya rabauta, wanda kuma ya yi tuntuɓe (da marar hali) to ba shi da haƙƙin ɗaukar fansa”.

Don haka wanda ya samu mace ta gari sai ya gode wa Allah maɗaukaki, amma wanda bai samu ta gari ba to ba shi da haƙƙin ɗaukar fansa don ta munana masa, sai ya ɗauki bargon haquri ya yafa, sai dai wannan ba yana nufin ƙin ɗaukar matakin gyara ba kamar yadda zamu gani a wasu ruwayoyin.

Wassalam.

Daga Mustapha Musa Muhammad, 09123302968.