A tuna da matasa a rabon muƙaman sabuwar gwamnati

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Matasa wani muhimmin jigo ne a harkokin siyasa, don suna taka muhimmiyar rawa wajen ƙara wa siyasa armashi. Su ne kan gaba a yaƙin neman zaɓe, da gudanar da ayyukan zaɓe da suka haɗa da aikin sa ido don wakiltar jam’iyyu, aikin tafiyar da zaɓe, har ma da shiga bangar siyasa. Kar ku manta hatta manna fostar ɗan takara matasa ne ke yi.

A wasu wurare da dama, da zarar ɗan takara ya yi shirin bayyana aniyarsa ta neman wani muƙamin siyasa to, matasa na daga cikin rukunin farko da yake fara ganawa ko neman shawarar su da goyon bayan su. Har wasu kwamitoci na matasa ake kafawa don raba ayyukan da ake sa ran matasan za su gudanar, domin taimakawa ɗan takara samun nasara.

Wasu har wayoyi ake saya musu a sa musu data, don su riqa rubuce-rubuce na yaɗa manufa ga jama’a a zaurukan sada zumunta, suna zaburar da sauran matasa da razana ’yan adawa ta cikin rubutun da suke fitarwa. Matasa ne suke ayyukan yaɗa manufofin ɗan takara ta cikin waqoqin siyasa da wasannin kwaikwayo ko shirya gangamin matasa iri iri ana gudanar da gasa da wasannin motsa jiki, don ƙara jan hankali.

Babu wata harkar siyasa da za ta gudana ba tare da matasa ba, saboda su ne masu jini a jika, su ne ke da zafin nama, da sabbin tunani, dabaru da rashin tsoro. A duk siyasar da aka ga cincirindon matasa ko maza ko mata a ciki, babu shakka za a ga kutsawarta da karvuwarta a lungu da saƙo daban ne. Sai dai ba kasafai matasan suke samun damar cin moriyar wahalhalun da suke yi wa siyasa ba.

Yawanci daga an ce an samu nasara, ’yan siyasar da suka goyawa baya sun shiga ofis to, sai ka ga an ajiye waɗannan matasa a gefe. Babu ayyukan yi, babu romon dimukraɗiyyar da aka yi musu alqawarin za su kurɓa. Kuma babu su a cikin muƙaman da ake rabawa waɗanda suka yi wa jam’iyya wahala. Ko da waɗanda ake bai wa muqamin jeka-na-yi-ka, na masu taimakawa na musamman, irin su S.A da P.A, za ka ga ba wani aikin a zo a gani suke yi ba.

Ga duk wanda ya lura da yadda aka gudanar da hidimar yaƙin neman zaɓe a dukkan zaɓukan da suka gabata na 2023, zai lura da dafifin matasa da cikowarsu a duk wani gangami ko taron siyasa da aka shirya. Ƙungiyoyin matasa iri-iri, ciki har da ’yan wasan Hausa da mawaƙa da marubuta daga sassan Nijeriya daban daban, duk sun fita sun bayyana goyon bayansu da gudunmawar su.

Ba kawai a ƙarƙashin Jam’iyya mai mulki ba, har a sauran jam’iyyu. Za a iya cewa wannan zave ne na mata da matasa zalla, domin dattijan da suka jagoranci tafiyar da zave ba su taka kara sun karya ba.

Sai dai yanzu da Allah ya sa aka samu nasarar gudanar da zavuka cikin nasara, waɗanda suka samu nasara suka karɓi rantsuwar kama aiki, har ma an fara naɗe naɗen muƙamai, mun sa ran ganin sauyi daga irin yadda ’yan siyasa na baya suka yi.

Amma da alamun za a koma gidan jiya, daga irin rahotannin dake fitowa daga wasu jihohi har yanzu dai ba ta canja zani ba. Abin takaici ne yadda aka kasa canja salon labarin da aka saba ji, wato an gagara cika alƙawuran da aka yi wa matasa.

Sunayen da muka fara ji ana fitarwa don naɗen-naɗen sabbin kwamishinoni da masu riƙe da wasu muhimman muƙamai a fadar gwamnati, duk babu matasa. A inda kuma aka ji an ambaci sunayen matasa za ka samu ba wasu su da wani tasiri ba ne.

Mun sani ba kowanne muƙami ne za a ɗauko matasa a ba su ba, akwai ayyukan da ke buƙatar dattijo ko babban ma’aikaci wanda ya jima a aiki kuma yake da gogewa da sanin makamar aiki. Amma kuma su ma matasan akwai ayyukan da za a iya basu gwargwadon iliminsu da ƙwazon su a ayyukan da suka yi wa jam’iyya ko cikin al’umma.

Wata matashiya Gimbiya Zainab Zakariyya na ganin tun daga yanzu ne za a fara ɗora matasa a wuraren da aka san za su yi wa al’umma aiki, don su fara sanin madafar aiki da samun gogewar da ake buƙata saboda gaba. Idan har ba a ja su an tafi da su a sha’anin gudanar da mulki ba, sai yaushe za su iya har a yarda suna da gogewar da za ta sa a ba su wani muƙami?

Ahmad Abubakar, wani shugaban ƙungiyar matasa ne da suka yi hidima don samun nasarar sake zaɓen Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana fatan sa na ganin wahalar da matasasuka sha wajen kafuwar gwamnati mai ci ba za ta tafi a banza ba.

Gwamnati za ta duba ta ga me ya dace a yi musu, don a ramawa kura aniyarta. Tunda dai dama kowa na yin siyasa ne saboda ya amfana da ribar dimukraɗiyya, domin haka su ma bai kamata a yi watsi da buƙatunsu ba!

Aisha Abdulhamid na daga cikin matasan da suka yi hidima wajen yaƙin neman zave a zaurukan sada zumunta, ita ma kuma fatan da take yi shi ne a tuna da matasa wajen gudanar da tsare-tsaren gwamnati.

Kamar yadda suka riqa yaɗa manufofin ’yan takara da abubuwan da suke so su yi a yaƙin neman zave, ya kamata a wannan lokaci da aka samu nasara a yi musu abin da za su ji daɗi don rayuwarsu ta gaba ta yi kyau. Ta ce, matasa na buƙatar tallafin karatu da ayyukan yi, jarin sana’o’in dogaro da kai, da muqaman gwamnati ga waɗanda suka cancanta.

Duk da kasancewar a Nijeriya ’yan siyasar da suka shahara kuma suka daɗe ana damawa da su basu cika son, jawo ƙananan ’yan siyasa a jiki ba, in dai ba ’ya’yan su ko makusantansu ba, sun fi son a ce koyaushe su ne suke yi. Amma ta yaya tafiyar tasu za ta yi kyau idan babu matasa a kusa da su? Ko da yaran da suke bai wa kayan shaye-shaye su je cibiyar zaven da suke ganin ba su ne ke samun rinjaye ba, don su haifar da yamutsi a soke zaɓen wajen.

Ko masu zuwa satar akwatin zaɓe da kai wa abokan adawa hari, ai duk matasa ne, kuma su ma suna da burin zama wani abu a rayuwarsu. Idan da suna aiki da hankali da wayo, ai kamata ya yi su gyara rayuwar waɗannan yara, ta yadda watarana su ne za su taimaka musu a siyasance ko a zamantakewar rayuwa ta yau da gobe.

Babu al’ummar da ta ke wasa da makomar matasanta sai, sai wacce ba ta san nauyin da ya rataya a wuyanta na gina al’umma da raya ƙasa ba. A daidai nan ne nake so in yabawa sabon Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf bisa yadda ya fara nuna aniyarsa ta gyara makomar matasan jihar.

Musamman dangane da cibiyar da aka farfaɗo da ita na gyara tunanin matasa masu shaye-shaye da ƙwacen waya, da biyan kuɗaɗen jarabawar ɗaliban Jihar Kano masu kammala babbar sakandire ta NECO, tare da shirin dawo da ɗaukar nauyin karatun ɗaliban da suka samu sakamako mai kyau na First Class, a matakin Digiri na farko, don zuwa ƙasashen waje ƙaro ilimi. Wannan abin a yaba ne sosai.

Muna fatan cikin sabbin naɗe-naɗen da za su biyo baya za mu ga cincirindon matasa da mata ’yan boko da suka taka rawar gani wajen kafuwar wannan gwamnati, don su ma su zo su ba da tasu gudunmawar.

Ba a Jihar Kano kaɗai ba, muna sa ran ganin kwamishinoni matasa, daraktoci matasa, manyan shugabannin hukumomi matasa, a dukkan jihohin Nijeriya. Sannan tare da kira da jan kunnen duk matashin da Allah Ya sa yana da rabo a wannan gwamnati to, lallai ya yi abin da ya dace, kada ya ba mu kunya. Kuma shi ma ya jawo wasu ’yan uwansa matasa da za su taya shi aikin raya ƙasa tare.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *