Daga BASHIR IBRAHIM NA’IYA
Guraren koya sana’o’i mallakin jahar Kano waɗanda Kwankwaso ya gina, da a ce gwamnatin da ta wuce ta dora an ci gaba da koya wa matasa sana’o’i a guraren tsawon shekara 8 din Ganduje da yanzu wata maganar a ke yi ba wannan ba.
Domin in kuka kwashe shekaru 8 daga cikin shekarun yaran da ake kamawa da laifin sata ko fashin waya, za ku ga duk ba su wuce shekara 10 ba zuwa 12 ba a wancan lokacin.
Kamar yadda wani ya ke gaya min, ya je wuraren koyar da sana’o’in da Kwankwaso ya giggina, ya cemin ya yi takaici kwarai da gaske ganin yadda gwamnatin da ta wuce ta yi watsi da wajen duk injina da na’urorin da Kwankwaso ya zuba duk sun lalace sun yi tsatsa wuraren sun koma kamar daji.
Waje ɗaya da ya tsira shi ne, inda ake koyan yin takalma, shi ne kaɗai ya tsira, ni kaina mun tura yara 4 mun biya musu komai sun koyi yadda ake hada takalma, biyu daga cikin yaran yanzu suna nan suna ta sana’arsu ta yin takalman, ɗaya ma kasuwa ya koma suka buɗe shago.
To me kuke tsammani da a ce duk guraren koyan sana’ar nan tsawon shekaru 8 na gwamnatin Ganduje ba ta yi watsi da su ba, shin za mu samu kanmu cikin wannan matsalar?
Ko za a samu zai zo da sauki ba kamar yadda yanzu muke ganin dandazon yara ‘yan 16 zuwa 20 suna yin sata da fashin waya ba. An bar kari tun ran tubani, a dai yi duba na tsanaki akan matsalar nan.
Bashir Ibrahim Na’iya masani ne kuma mai sharhi a kan al’amuran yau da kullum. Ya rubuto daga Maryland ta USA.