A yi hattara da kiraye-kirayen kare kai

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Jihar Filato da ke tsakiyar Nijeriya ta sake shiga kanun labarai a kafafen sadarwa daban-daban cikin watan da ya gabata, sakamakon wasu sabbin hare-hare da suka auku a babban birnin jihar, wato Jos. A dalilin wata rikita-rikita mai nasaba da ƙabilanci da addini, wacce aka jima ana yi tsawon shekaru fiye da 20, inda aka samu asarar ɗimbin rayuka da dukiyoyi da har yau ba a gama tantance adadinsu ba.

Labari na baya bayan nan nan da ya fi ɗaukar hankali daga jihar shi ne, taron manema labarai na duniya da Majalisar Dokoki ta Jihar Filato ta gudanar a ranar Juma’a ta makon da ya gabata, inda ta yi maganganu masu kaushi game da abubuwan da ke faruwa a jihar na taɓarɓarewar tsaro. A ciki har da zargin gazawar gwamnati da jami’an tsaro wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’ar jihar, tare da kira ga al’ummar jihar su tashi su kare kansu daga maƙiyan Filato, masu neman yi musu kisan ƙare dangi don su ƙwace musu ƙasa.

Babban abin da ya fi ɗaukar hankalina har nake son yin sharhi a kai shi ne, batun kowa ya tashi ya kare kansa, da ya zama babban labarin da jaridu da kafafen sadarwa suka riƙa ɗauka da kururutawa, har ma kuma ya jawo zazzafan martani daga ɓangarori daban-daban, har ma da gwamnatin jihar, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Simon Lalong, Shugaban Majalisar Gwamnonin Arewa.

Kamar abin haɗin baki, sai ga wasu qungiyoyin ƙabilu da na addini su ma sun kwaikwayi wannan barazana, suna ƙara tunzura jama’ar jihar a ɗauki makamai a kare kai. Na baya bayan nan, ita ce ƙungiyar matasan Kiristan Nijeriya ta YOWICAN, wacce ita ma ta fito ta nuna gazawar jami’an tsaro wajen kare rayukan al’umma, musamman a Jihar Filato.

Ko da yake ba yanzu ne aka fara samun irin wannan kira na kare kai a Jihar Filato ba, tun a shekarun baya lokacin gwamnatin da ta shuɗe ƙarƙashin tsohon Gwamnan Jihar Jonah David Jang, yayin da hare hare suka tsananta a kan mazauna ƙauyuka a ƙananan hukumomin Riyom da Barikin Ladi, a rikicin da makiyaya da manoma suka riqa fama da shi a yankin. Masu faɗa a ji a jihar sun riƙa yin irin wannan kiran ga jama’arsu, na a tashi a kare kai, saboda abin da a wancan lokacin suka kira mayar da su saniyar ware da Gwamnatin Tarayya ta yi game da wannan matsala da ta daɗe tana damun yankin.

Ko bayan matsalar tsaro a Jihar Filato, akwai rahotannin da suka ɗauki hankalin ‘yan Nijeriya a watannin baya yayin tsanantar hare haren ‘yan bindiga da masu satar mutane a tsakanin jihohin Katsina da Zamfara, nan ma an jiyo gwamnonin jihohin a wasu rahotanni daban-daban, suna kira ga al’ummar ƙauyukan da suka fi fuskantar matsalar ta’addancin ‘yan bindiga cewa, su ma su tashi su kare kansu, kar su riƙa bari ana yi musu kisan kiyashi ba tare da sun samu ɗaukin gaggawa daga jami’an tsaro ba.

Kenan za mu iya cewa, wannan kiraye-kirayen da wasu mahukunta da masu faɗa a ji ke yi wa wasu ‘yan Nijeriya na su tashi su ceci rayuwar su, saboda gazawar jami’an tsaron ƙasa ba yanzu aka fara ba. Kuma za a iya cewa ma ya fara zama gama garin magana a wuraren da ta’addanci da rikice-rikice suka yi tsamari.

A yayin da wasu ke ganin tilas ce ke sa wasu yin irin wannan furuci ga raunanan talakawansu waɗanda ba su da ƙarfi da gogewar yin fito na fito da masu riƙe da muggan makamai da ƙeƙasasshiyar zuciya. Wasu na ganin yin waɗannan kalamai a yayin da lamura suka rincaɓe, babbar gazawa ce ga hukumomi, sannan barazana ce mai ƙarfi ga sha’anin tsaron ƙasar nan. Duk da yake muna sane da cewa, jami’an tsaron ƙasar nan suna fuskantar manyan ƙalubale masu yawa da suka haɗa da bazuwar ƙungiyoyin ta’adda da ƙarancin jami’an tsaro da rashin isassun kayan aiki na zamani, da za su taimaka wajen kai ɗaukin gaggawa cikin dazuka da ƙauyuka da ke da nisa da kwazazzabo, domin daƙile hare haren ‘yan bindiga.

Wannan ta sake dawo da muhawarar da aka daɗe ana yi a tsakanin gwamnonin Nijeriya, ta batun samar da ‘yan sandan jihohi, saboda ƙorafin da gwamnonin suke yi na rashin ba su ƙarfin iko kan jami’an tsaro, kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasa ya gindaya. Don haka suke kukan matuƙar ana son su yi abin da ya kamata kan sha’anin tsaro a jihohin su, tilas a tabbatar musu da ikon da suke da shi na shugabancin tsaro a jihohin su. Suna son ya zama su ne ke da ikon bayar da umarni kan yadda sha’anin tsaro zai kasance a jihohin su, ba lallai sai sun nemi sahalewar Shugaban Ƙasa ba.

Wannan wani muhimmin batun ne na daban da nan gaba za mu iya tattaunawa a kai. Amma a yanzu ina son mu mayar da hankalin mu ne kan ƙalubalen da Nijeriya za ta iya samun kanta a ciki idan muka ci gaba da ganin ba laifi ba ne, kowa ya ɗauki matakin kare kansa, saboda muna ganin gazawar jami’an tsaron mu wajen kare rayuka da dukiyoyin ‘yan uwan mu. Ba ma tunanin haɗarin da hakan zai iya haifar wa ƙasar nan nan gaba, sakamakon bazuwar makamai hannun ‘yan ƙasa.

Ashe ba za mu yi aiki da hankali ba wajen nazarin wasu hanyoyin da za su iya kawo sauƙi wajen magance wannan matsala ba, kamar horar da matasa ‘yan sa kai da za su yi aiki ƙarƙashin kulawar jami’an tsaron gwamnati da ba da gudunmawa wajen tunkarar ta’addanci a ƙauyuka da lunguna ba, kamar yadda yake faruwa a Jihar Borno game da ayyukan ‘yan ƙato da gora. Mai ya sa ‘yan siyasar mu da masu irin waɗannan maganganu na nuna gazawar jami’an tsaron mu ba za su yi tunanin illar da kalaman su za su yi wa al’umma ba.

Mun manta da Laberiya ne, ko ba mu ga illar irin hakan a ƙasashen Libiya da Siriya ba ne!

Lallai hukumomin tsaron Nijeriya su tashi tsaye su yi maganin masu irin waɗannan kalamai, domin haɗarin da suke so su jefa ƙasar nan a ciki. Sannan su fitar da dabaru daban-daban na yadda za su inganta tasirin su, wajen tattara bayanan sirri. Ƙwarin gwiwar su wajen tunkarar duk wata ƙungiyar ta’addanci da masu mugun shiri a ko ina suke a ƙasar nan. Da samar da horon da ya dace ga matasan da aka tantance kuma aka yarda da kishin su ga cigaban ƙasar nan, domin koyar da su yadda za su ba da gudunmawa a samar da ingantaccen tsaro a ƙasar nan. Lallai kada a bar wannan aikin a hannun ‘yan siyasa da ƙungiyoyin kare muradun wata ƙabila.

Lallai ne gwamnonin ƙasar nan da shugabannin al’umma su ajiye siyasa a gefe, a daina wasa da rayukan ‘yan ƙasa waɗanda ke wahala wajen kaɗa musu ƙuri’a da neman abin da za su rufa wa kansu asiri. Su tsaya su fuskanci yadda za a kawo ƙarshen waɗannan fitintinun da suke haifar da asarar rayukan bayin Allah, su haɗa kai da jami’an tsaro da Gwamnatin Tarayya, wajen fitar da dabaru na zamani da za su inganta harkar tsaro a ƙasar nan.

Ba daidai ba ne, mu riƙa zubar da kima da mutuncin jami’an tsaron ƙasar mu a idon sauran ‘yan ƙasa da duniya ba. Sojoji da sauran rundunonin tsaro na ƙasar nan, kamar yadda na tava faɗa a wannan shafi, su ne garkuwar Nijeriya. Har yanzu ƙarfi da tasirin su na nan, wajen iya tunkarar kowanne ƙalubale da ke addabar ƙasar nan, daga ciki ko daga waje. Duk da ƙalubalen da suke fuskanta a irin nasu tsarin, haƙƙin mu ne mu ba su goyon baya da ƙwarin gwiwa.

A ƙarshe, ina mai shawartar hukumomi a Jihar Filato, musamman Majalisar Dokoki ta Jihar, su sake bitar ƙudurorin da suka fitar a taron manema labarai da suka gabatar, inda suka buƙaci kowacce ƙaramar hukuma daga cikin 17 da ke jihar su kafa rundunar ‘yan banga ta mutane 200 da za su riqa kula sha’anin tsaro a yankunan su. Yayin da muke yabawa da wannan yunƙuri muna kuma jan hankalin ‘yan siyasar jihar su guji cusawa jama’ar su ƙiyayyar jami’an tsaro, suna nuna kamar duniya ba ta ƙaunar su, su ne kawai za su yi wa kansu komai. Wannan babban kuskure ne.

Babu wata jiha a qasar nan da za ta ji cewa, ba ta ƙarƙashin kariyar rundunar tsaron Nijeriya, ko ta fi ƙarfin yin biyayya ga abin da zai kawo tsaro ga rayuwar kowanne ɗan Nijeriya. Ƙasar nan tamu ce baki ɗaya, kuma dole mu haɗa kai don ceto ta daga maƙiya son zaman lafiya.