AAPC ta buƙaci jam’iyyun siyasa da su haɗa kai da Tinubu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ƙungiyoyin goyon bayan jam’iyyar AAPC sun yi kira ga jam’iyyun siyasa da su rungumi haɗin kai da ’yan uwantaka da Bola Ahmed Tinubu, zaɓaɓɓen shugaban ƙasa ya yi musu.

Darakta Janar na ƙungiyar, Dakta Kailani Muhammad, ne ya yi wannan kiran a ranar Talata a wajen wani taron Leadership of APC Grassroots Independent Campaign Council a Abuja.

Muhammad ya buƙace su a matsayinsu na ’yan Nijeriya masu kishin ƙasa da su haɗa kai da Tinubu wajen gina ƙasa domin ciyar da ƙasa gaba.

“Muna kira ga jam’iyyun adawa, PDP, Labour Party da mambobinsu da su karɓi hannun zumunci da ’yan uwantaka da babban jagoranmu, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya yi musu.

“Mun ga shugabannin jam’iyyar PDP da mambobinsu sun yi fito-na-fito a kan titunan Abuja, suna wulaƙanta kansu bayan sun garzaya kotu domin ƙalubalantar zaven shugaban ƙasa.

“Tuni sun garzaya kotu kuma ta ba su takardar cewa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC ta ba su takardar sakamakon zaɓen, wanda INEC a shirye ta ke ta yi.

“Muna farin ciki a cikin gida a Nijeriya cewa kowa da kowa ya goyi bayan zaɓen shugaban ƙasa na ranar 25 ga watan Fabrairu inda Tinubu da Shettima suka fito a matsayin waɗanda suka yi nasara.

“Ya kamata su sani cewa ba maguɗi bane, amma zaɓe ne kuma shi ya sa ma ƙasashen duniya suka tabbatar da cewa an gudanar da zaɓen cikin gaskiya da adalci,” in ji shi.

Babban daraktan ya ce, an tura ƙungiyoyi daban-daban a wannan dandalin zuwa jihohi 28 domin tabbatar da samun nasara a zacukan gwamnoni da na ’yan majalisar jiha na ranar 11 ga Maris.

“Mun kuma kafa kwamitoci da za su zagaya jihohi 28 kamar yadda muka yi a zaven shugaban ƙasa da na ’yan majalisun tarayya da ya gabata.

“Mun tura su zuwa ga dukkan runfunan zaɓe 146,000 a Nijeriya,” in ji shi.

A nasa jawabin, Mista Silas Agara, Kodineta na ƙasa, APC Grassroots Independent Campaign Council, ya ce maƙasudin taron shi ne haɗa kan ƙungiyoyin goyon bayan APC daban-daban.

A cewarsa, taron na da nufin inganta haɗin kai, haɗin kai, fahimtar juna, tsakanin ƙungiyoyin goyon bayan APC.