Abba Gida-gida ya gayyaci al’umma zuwa shaida karɓar shaidar lashe zaɓen Gwamnan Kano

Daga RABI’U SANUSI a Kano

Zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kano ƙarƙashin jam’iyyar NNPP, Engr. Abba Kabir Yusuf, ya gayyaci al’ummar jihar Kano da kewaye zuwa inda Hikunar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, za ta miƙa masa shaidar lashe zaɓen Gwamnan Kano tare da mataimakinsa, Kwamred Abdulsalam Gwarzo.

Ranar Laraba ake sa ran INEC za ta miƙa wa waɗanda suka lashe zaɓen gwamna a jihohinsu shaidar lashe zaɓen.

Gayyatar Abba Gida-gida na ƙunshe ne cikin sanarwa da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ga manema labarai a ranar Talata.

Sanusi Bature ya ce gangamin karɓar shaidar zai gudana ne Sakatariyar hukumar zaɓe da ke Kano.

Sanarwar ta bayyana cewa zaɓaɓɓen gwamnan na Kanon ya buƙaci magoya bayan jam’iyyar NNPP da dukkan masoya da su zama masu bin doka da oda yayin gangamin.

Taron zai gudana ne da misalin ƙarfe 10:00 inda ake sa ran samun mahalarta daga ciki da wajen Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *