Abba Gida-gida ya yi miƙa saƙon goron sallah ga Kanawa

Daga RABI’U SANUSI a Kano

Gwamnan Jihar Kano mai jiran gado, Engr. Abba Kabir Yusuf, ya miƙa daƙon taya al’ummar Jihar Kano murnar kammala azumin watan Ramadan na bana.

A cikin saƙo nasa, Abba Kabir ya buƙaci al’umma a cigaba da ɗabbaƙa kayawawan darussan da aka koya yayin watan azumin da ya ƙare.

Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar juma’a.

Sanarwar ta ce: “Ina tabbatar wa Jama’ar Jihar Kano cewa gwamnati mai jiran gado ƙarƙashin jagorancina za ta samar da hanyoyin da za su taimaka wa al’ummarmu a fannoni daban-daban.

“Ina amfani da wannan dama wajen jan hankalin al’ummarmu da a guji tuƙin ganganci da sauransu.”

A ƙarshe, Kabir Yusuf ya yi kira ga Kanawa da su zama masu son juna da zaman lafiya, tare da yi wa jihar addu’o’in samun cigaba mai ɗorewa.