Abba Kyari: Abokin harƙallar Hushpuppi, Woodberry ya amsa laifin zamba

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Shahararren ɗan damfara ta yanar gizo kuma amini ga Hushpuppi, Olalekan Jacob Ponle, wanda aka fi sani da ‘Woodberry’, kuma ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi da aikata almundahanar kuɗi tare da gawurtaccen ɗan sandan Nijeriyan nan, ACP Abba Kyari, a Amurka, ya amsa laifin damfarar mutane ta wayar tarho, sannan ya kuma amince ya biya Naira biliyan 3.6 (dala miliyan 8) tare da miƙa motoci da agogonni ga gwamnatin ƙasar waje.

Woodberry, sanannen abokin ɗan damfaran yanar gizo ne da ake tsare da shi yanzu, Ramon Abbas, wanda aka fi sani da Hushpuppi, a kwanan baya a cikin wata sanarwa da ya shigar a gaban Kotun Lardi na Arewacin gundumar Illinois ta Gabas a ranar 6 ga Afrilu, ya amsa laifin tuhumar da ake masa.

A bisa yarjejeniyar da ya shigar, ana buƙatar ya mayar da kuɗaɗen da suka kai dalar Amurka miliyan 8 da ya zambaci wasu kamfanoni bakwai.

“Wanda ake tuhuma ya fahimci cewa ta hanyar amsa laifinsa, zai ba wa Amurka duk wata dama akan kadararsa,” in ji shi.

Manyan motoci sun haɗa da Rolls Royce Cullinan ma mai lamba J9153, Lamborghini Urus (N4973) da Mercedes-Benz G-class (G68816).

Sauran kayayyakin da aka kama sun haɗa da agogon Rolex guda huɗu, agogon Patek Philippe ɗaya, agogon Audemars Piguet guda uku, ‘yan kunne masu launin zinari da lu’u-lu’u uku, da sarƙoƙin wuya na zinare guda shida.

A bara, ya yi asarar 151.8 na Bitcoin ga gwamnatin Amurka. A ranar 10 ga Yuni, 2020, an kama Woodberry a Dubai tare da Ramon Hushpuppi Abbas, wanda a halin yanzu ke zaman ɗaurin shekaru 11 a kan laifin zamba.

Kafin kama shi, Woodberry ya shahara da yin rawa da kuma nuna tsadar kayan sawa da kuma nuna dukiyarsa ta haramtacciyar hanya ga ɗimbin mabiyansa na Instagram, wazanda galibinsu ba su da masaniyar irin yadda ya yi rawa waɗannan dukiya.