Abduljabbar: Za mu ɗaukaka ƙara kan hukuncin kisa – Ƙungiya

Daga IBRAHIM HAMISU, Kano

Wata ƙungiya ƙarƙashin ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta Alhaƙƙu ta bayyana shirinta na ɗaukaka ƙara kan hukuncin kisa da kotun shari’a ta yanke wa Sheikh Abduljabbar Kabara bisa samunsa da laifin ɓatanci.

Yayin da yake jawabi ga manema labarai a ranar Juma’a a Kano, shugaban ƙungiyar Sa’id Bn Usman, ya bayyana cewa ƙungiyar ta tattaunawa da iyalai da makusantan malamin kan batun, kana daga bisani sun yanke shawarar ɗaukaka ƙara domin tabbatar da adalci.

Ya ƙara da cewa, ƙungiyar ba ta gamsu da hukuncin ƙaramar kotun ba.

A cewarsa, an kammala shirin ɗaukaka ƙarar nan bada jimawa ba, kuma za a sanar da al’umma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *