Abdulrazaq ya sake lashe zaɓen gwamnan Kwara

Daga SANI AHMAD GIWA

Hukumar Zaɓe a Jihar Kwara ta sanar da AbdulRahman AbdulRazaq a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamna da ya gudana a ranar Asabar.

Hakan na nufin ya samu wa’adin mulki na biyu kenan.

AbdulRazaq na Jam’iyyar APC ya doke Alhaji Shuaib Yaman Abdullahi na Jami’yyar PDP da kuma Alhaji Hakeem Oladimeji Lawal na SDP.

Babbar jami’in da ke lura da zaɓen wato Farfesa Isaac Itodo ya bayyana cewa gwamnan ya samu nasara a duka qananan hukumomi 16 na faɗin jihar.