Abin ban mamaki! Ƙirƙirar fasahar CMG ta haskaka wasannin Olympics na lokacin hunturu!

Daga CMG HAUSA

Kwanan baya, kwamitin wasannin Olympic na ƙasa da ƙasa ya aike da wasiƙa zuwa babban rukunin rediyo da talabijin na ƙasar Sin wato CMG a takaice, inda ya nuna yabo da godiya ga nasarar da ya samu, wajen watsa shirye-shirye kai tsaye, yayin wasannin Olympics na lokacin hunturu da aka shirya a birnin Beijing, da kuma yadda yake yada wasannin Olympic na ƙasa da ƙasa yadda ya kamata.

A matsayinsa na gidan rediyo da talabijin na ƙasa mai masaukin baki, kuma abokin haɗin kai na kwamitin wasannin Olympic na ƙasa da ƙasa, a aikin watsa shirye-shirye kai tsaye ta kafar talabijin, CMG ya dogara da tsarin dabarun fasahar “5G+4K/8K+AI”, tare da babbar fasahar watsa shirye-shirye ta 4K / 8K dake jagorantar duniya, da manyan na’urorin ɗaukar bidiyo na fasaha da ya yi nazari da kansa, da kuma fitattun masu ba da tabbaci kan fasahar watsa shirye-shirye kai tsaye, don cimma maƙasudin “Wasannin Olympics na fasaha, da amfani da fasahar 8K don kallon wasannin Olympics.”

Kana ya karya ingantaccen matsayin bajintar sadarwa, na sama da mutane biliyan 62.814 da suka kalli wasannin Olympics na hunturu, ta hanyar amfani da dandamali daban daban na CMG.

Mai fassara: Bilkisu