Abin da raguwar farashin kayan abinci ke nufi – Ƙungiyar Arewa

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Ƙungiyar Arewa Think Tank (ATT) ta ce raguwar da aka samu a farashin kayan abinci a faɗin kasar nan, musamman a Legas da Abuja, ya nuna cewa manufofin tattalin arzikin Shugaba Bola Tinubu na haifar da sakamako mai kyau.

A cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar ta ATT, Muhammad Alhaji Yakubu ya fitar, ya ce duk da ci gaban da aka samu, ‘yan Nijeriya da dama na ci gaba da sukar shugaban ƙasar maimakon yabawa da ci gaban da aka samu.

“Mun kasance muna roƙon ‘yan Nijeriya da su yi haƙuri da Shugaban ƙasa, kuma a yau, mun yi farin ciki da cewa shawararmu ba ta kasance a banza ba. A yanzu mutane suna ganin canje-canje masu kyau a cikin yanayin zamantakewa da tattalin arzikin kasar,” inji sanarwar.

Ya buƙaci ‘yan Nijeriya da su ƙara haƙuri, yana mai ba su tabbacin cewa za a kara samun ci gaba a cikin watanni masu zuwa.

“A karon farko tun lokacin da Shugaba Tinubu ya hau mulki a watan Mayun 2023, matsalar tsadar rayuwa ta Nijeriya ta fara yin sauƙi. Wani binciken kasuwa da aka yi kwanan nan a Legas, cibiyar tattalin arzikin ƙasa, ya nuna raguwar farashin kayan masarufi masu muhimmanci, yana sauƙaƙa nauyin kuɗi a kan ’yan Nijeriya masu fafutuka waɗanda ke fama da hauhawar hauhawar farashi tun bayan barkewar cutar ta COɓID-19,” inji shi.

A cewar ATT, binciken ya nuna cewa buhun shinkafar ƙasar waje mai nauyin kilogiram 50 a yanzu ana sayar da shi kan N85,000, inda ya ragu da N110,000 watanni biyar da suka gabata, yayin da shinkafar gida ta ragu zuwa N95,000 daga N105,000 a cikin watanni uku. Farashin babban kwandon tumatur ya faɗi sosai daga N120,000 zuwa N35,000, wanda ya nuna an samu raguwar kashi 70 cikin ɗari.

Yakubu ya ce raguwar farashin kayan abinci na ƙara wa masu ƙaramin ƙarfi sauƙi, domin ya inganta abinci a gida.

Sai dai ya yi kira ga gwamnati da ta tabbatar da cewa wannan al’amari ya ɗore tare da miƙa shi ga sauran kayayyakin masarufi.