Abin da ya sa Fulani makiyaya ke riƙe bindiga, inji Gwamna Bala

Daga FATUHU MUSTAPHA

Gwamnan Jihar Bauchi Sanata Bala Mohammed, ya ce Fulani makiyaya kan riƙe bindiga ne saboda kare kai.

Gwamnan ya faɗi a haka ne a lokacin da yake magana a wajen taron bikin Makon ‘Yan Jarida wanda Reshen Wakilai na Ƙungiyar ‘Yan Jarida a Jihar Bauchi ya shirya.

Ya riƙe bindiga kan taimaka wajen hana ɓarayi su kai musu hari su kashe su sannan su yi gaba da shanunsu.

Yana mai cewa gazawar gwamnati wajen bai wa makiyayan kariya shi ya ya sa su kuma suka ɗauki matakin kare kansu daga ta’addancin ‘yan ta’adda.

“Saboda shi Bafulatani mutum ne wanda ba ya zama wuri guda, yana shiga kurmi-kurmi, ya sha haɗuwa da ɓarayin shanu masu ɗauke da bindigogi su kashe shi sannan su awon gaba da dukiyarsa (shanunsa).

“Ba shi da zaɓi da ya wuce riƙe bindiga saboda al’umma da gwmnati sun gaza ba shi kariyar da yake buƙata, don haka mene ne laifinsa a nan, laifin na gwamnati da al’umma ne.

“Ba daidai ba me a haɗa baki ɗaya a yi musu kuɗin goro game da aikata manyan laifuka, domin a cikin kowace ƙabila akwai ɓata-gari”, inji Bala Mohammed.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *